Oluwatobi Ajayi, Shugaba kamfanin Nord Automobiles, an karrama shi da shaidar yabo ta Leadership, saboda irin gagarumar gudunmawar da ya kw bayarwa ga masana’antar ƙera motoci ta Nijeriya.
An haifi Ajayi, a shekarar 1988, ya halarci makarantar sojojin ruwa ta Najeriya tun daga matakin firamare har zuwa sakandare. Ya yi digiri a fannin kimiyyar ƙasa da aikin gona a jami’ar Olabisi Onabanjo, Ago-Iwoye.
- Kasar Sin Za Ta Yi Garambawul Da Bullo Da Sabon Ci Gaban Kasuwancin Fasahohin Zamani
- Ma’aikatar Kasuwanci Da Zuba Jari Ta Gudanar Da Bikin Makon Abokan Cinikayya
Tun daga lokacin da ƙulla alaƙarsa da kamfanin ƙera motoci na Mercedes-Benz zuwa lokacin da ya kafa kamfaninsa na Nord Automobiles, ya yi nasarar ƙera motoci waɗanda darajarsu ta kai biliyan ₦4.2.
Ƙoƙarinsa da irin jajircewarsa wajen tafiyar da kamfanin Nord, wata alama ce babba da take nuna irin jajircewarsa da hazaƙarsa ga ‘yan Nijeriya a fannin kere-kere.
Manufar Ajayi, na samar da masana’antar ƙera motoci a Nijeriya da irin nasarar da kamfanin Nord ya ke samu ya sanya jaridar Forbes ta sanya sunansa cikin mutane masu kishi da burin samar da sana’o’in dogaro da kai a nahiyar Afrika a shekarar 2021.
Shugabancinsa da hangen nesansa ya sanya shi zama gwarzon Shugaban Kamfanoni masu zaman kansu na shekarar 2024 na jaridar Leadership.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp