Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya danganta matsalolin da Nijeriya ke fuskanta da haɗama, son kai, da kuma jahilci, yana mai cewa irin waɗannan ɗabi’un mutane ne suka hana cigaban ƙasar.
Yayin da yake jawabi a wajen bikin tunawa da cikar Cocin Methodist ta Nijeriya shekaru 40 a Abuja, Obasanjo ya bayyana cewa Allah ya albarkaci Nijeriya da yalwar arziki, amma mutanen ƙasar sun yi babakere wajen tafiyar da su.
- Yawaitar Juyin Mulki A Afirka Na Nuna Matasa Suna Neman Masu ‘Yanci – Obasanjo
- Zaki Ya Kashe Mai Kula Da Shi A Gidan Namun Daji Da Ke Dakin Karatu Na Obasanjo
Ya yi kira ga shugabanni da su rungumi sauyi na tunani da gyaran zuciya tare da yin kira ga cigaba da addu’o’i domin samun zaman lafiya da haɗin kai.
A wajen taron, Shugaba Bola Tinubu, wanda Ministan birnin tarayya Nyesom Wike ya wakilta, ya yaba wa Cocin Methodist bisa rawar da take takawa wajen ci gaban Nijeriya, musamman a fannin ilimi da adalci na zamantakewa.
Shugaban Cocin Methodist, Dr. Oliver Ali Aba, ya nuna godiya bisa juriya da cigaban da Nijeriya ta samu, inda ya jaddada buƙatar haɗin kai domin samar da al’umma mai cigaba, yana mai kira ga duk ‘yan ƙasa su hada kai don kyautata makomar ƙasar.