Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya yi gargaɗin cewa haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da babban barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban ƙasashen Yammacin Afirka.
Ya ce ya zama dole ƙasashen yankin su ɗauki satar ma’adinai da haƙar su ba bisa ƙa’ida ba a matsayin laifin ƙasa da ƙasa, saboda irin tasirin da yake da shi wajen haifar da rashin tsaro da koma-baya tattalin arziƙi.
- Ma’aikatar Kasuwancin Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Ta Shiga Tattaunawar Cinikayya Da Sahihiyar Zuciya
- Kotu A Kano Ta Tsare Wani Mai Gidan Marayu Bisa Zargin Satar Yara Da Safararsu Zuwa Delta
Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya faɗi haka ne a Abuja yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar Network of National Anti-Corruption Institutions in West Africa (NACIWA).
Shugaban ya nuna takaici cewa duk da shekaru da dama da ƙasashen yankin suka samu ‘yancin kai, cin hanci da rashawa da satar albarkatun ƙasa suna ci gaba da janyo koma-baya.
“Lokaci ya yi da za mu ɗauki satar ma’adinai da haƙar su ba bisa ƙa’ida ba a matsayin manyan laifuka na ƙasa da ƙasa, domin suna barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” in ji Tinubu.
Ya kuma roƙi shugabannin ƙasashen Yammacin Afirka su haɗe kai wajen yaƙi da ƙungiyoyi masu amfani da ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba, inda ya bayyana cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara haifar da tashin hankali da talauci.
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, shi ma ya yi kira ga ƙasashen yankin su amince da yarjejeniyar ECOWAS kan cin hanci, domin hana masu rashawa samun wajen ɓuya.
“Mu tabbatar babu inda ɓarayi za su ɓuya. Duk wanda yake tayar da hankali a ƙasashenmu bai kamata ya samu natsuwa ba,” in ji Fagbemi.
Ƙungiyar NACIWA ƙungiya ce ta hukumomin yaƙi da cin hanci daga ƙasashen ECOWAS, wadda ke aiki tare wajen yaƙi da rashawa.
Shugaban ƙungiyar na yanzu shi ne Ola Olukoyede, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar EFCC ta Nijeriya.