Ana fargabar aƙalla mutane biyar sun mutu sakamakon kifewar wani kwale-kwale a garin Ganta da ke Ƙaramar hukumar Buji a jihar Jigawa.
Haɗarin wanda shi ne na uku a jerin haɗuran kwale-kwale da aka samu a jihar cikin lokacin damunar nan ya laƙume rayukan fasinjoji biyar da ke cikinsa.
- Matsalar Kifewar Kwale-kwale A Jihar Jigawa
- Tinubu Zai Kai Ziyara Kasar Sin Domin Haɓaka Tattalin Arziki Da Kayayyakin More Rayuwa
Majiyoyin sun ce lamarin ya faru ne a jiya ranar Talata, yayin da kwale-kwalen ya isa yankin da ke kusa da ƙauyen Ganta da ambaliyar ruwa ta mamaye, inda igiyar ruwan ta mamaye kwale-kwalen da ke tafiya tare da nutsewa cikin ruwa.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin rundunar ’yansandan Jihar Jigawa, Lawan Shiisu Adam, ya ce sun yi ƙoƙari tare da sauran al’umma wajen gano gawarwakin fasinjojin da suka ɓace wanda jami’an lafiya suka tabbatar da mutuwarsu.
Lawan ya ƙara da cewa cikin fasinjoji akwai mata biyu da maza uku ciki har da yara ƙanana, dukkansu daga Malamawar Gangara, ƙaramar hukumar Birnin Kudu.