Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Erling Braudt Haaland ba zai sami damar buga wasan da Manchester City zata ziyarci Brighton a wasan mako na 29 da ya zama kwantai a watan jiya.
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Pep Joseph Guardiola ne ya bayyana haka ga manema labarai yayin daukar atisayen kungiyar gabanin wasan da zasu fafata a yau Alhamis a filin wasa na American Express Stadium da ke Brighton.
- PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor OsimhenÂ
- Shin Arsenal Ta Barar Da Damarta Ta Lashe Firimiya?
Haaland ya zama zakaran gwajin dafi a wasannin gasar Firimiya inda yanzu haka ya jefa kwallaye 20 a gasar, shine ya lashe kyautar takalmin zinare a kakar wasan da ta gabata da kwallaye 36.
City na fatan ganin ta doke Brighton a wasan yau domin matsowa kusa da masu jan ragamar gasar Firimiya Arsenal wadda ta yi wa Chelsea kaca kaca a makon jiya.