Kamfanin sadarwa ta MTN a Nijeriya ta ce ta katse layukan mutum miliyan 4.2 daga cikin turakarta, hakan na zuwa ne bayan da suka gaza hada lambar shaidar kasancewa dan kasa (NIN) da layukan wayoyinsu kafin zuwa karewar wa’adin ranar 28 ga watan Fabraru.
Idan za a tuna dai hukumar kula da harkokin sadarwa a Nijeriya (NCC) ta bayar da umarnin cewa, dukkanin kamfanonin sadarwa da suke Nijeriya, su tabbatar da cewa dukkanin mutanen da suke amfani da layukansu na sadarwasu da suka kasa hada lambarsu da shaidar NIN to kai tsaye a kullesu kafin ranar 28 watan Fabrairun 2024. Bugu da kari, daidaikun mutanen da suka mika lambar shaidarsu na zama.
- Ana Amfani Da Na’urar Hakar Mai Ta Zamani Da Kamfanin Sin Ya Kera A Uganda
- Kayayyakin Wasanni Kirar Kasar Sin Sun Samu Yabo A Gasar Wasannin Afirka Ta 13
‘Yan kasa NIN amma ba a samu lambar tantancewa ba, su kuma za a dakatar da layukan nasu ne ma gabaki daya. A gabar da aka hada layuka guda biyar ko fiye da lambar NIN da ba a tantance ba, lambar NIN din da aka gabatar ba tare da amincewa da su ba za a haramta amfani da su kafin ko zuwa ranar 29 ga watan Maris na 2024.
Kazalika, za a toshe layukan da suka hada lambarsu da NIN din da ba a tantance ba har sama da sau biyar zuwa ranar 15 ga watan Afrilun 2024.
Kafin a bude kowani layin da aka rufe, wajibi ne sai masu amfani da layukan su je a musu tantancewar zanen halitta kafin a saurari bude lambar tasu.
MTN a bayanin kudinta da ta fitar a ranar Juma’a ta ce, layukan da ta toshesu sun kasa gabatar da haidar kasancewarsu ‘yan kasa ne.
MTN a Nijeriya ta ce ta tantance layuka miliyan 19 tun lokacin da NCC ta bada umarni wa kamfanoni a watan Disamban 2023, da aka nemi su fara rufe layukan da ba su hada lambarsu da NIN ba. A cikin wannan adadin, layuka miliyan 4.3 an tantance kuma wasu miliyan 4.2 an katse su zuwa ranar 28 ga watan Fabraru a cewar MTN din.
Kamfanin ya kara da cewa, layukan da ya toshe su ba za su wani janyo wa kamfanin matsala kan kudaden shiganta ba domin kuwa ba wata daraja wajen samar wa kamfanin kudade suke ba.
Opay Ta Tabbatar Da Saukaka Wa Masu Amfani Hada Lambar Tantancewar Banki Da Shaidar Dan Kasa
OPay, cibiyar hada-hadar kudi, ta bai wa kwastomominta tabbacin cewa, za su samu sauki da hanzarin hade layukan tantancewarsu ta banki da lambar tantancewar kasancewa dan kasa NIN da asusun jiyarsa a dukkanin kafofinta domin taimaka wa kwastomominta gudanar da harkokinsu ba tare da wata damuwa ba.
Don haka ne, kamfanin ta bukaci dukkanin kwastominta da su gaggauta kasa cike dukkanin abubuwan bukata wajen hada lambobin tantancewar bankunansu da na shaidar NIN da asusun ajiyarsu.
Bisa ga tsarin babban bankin kasa CBN, Opay ta nemi dukkanin wani da bai kammala sabunta bayanan asusunsa ba, da ya tabbatar da yin hakan ta hanyar shiga cikin manhajar cibiyar gami da bin matakai da ka’idojin da aka gindaya domin sabunta bayanan asusunsu domin cin gajiyar cibiyar.
A wata sanarwa da aka fitar zuwa ga jaridar LEADERSHIP, wanda babban manajan gudanarwa na cibiyar hada-hadar kudi ta Opay, Dauda Gotring, ya ce, “Mun fahimci muhimmancin samar da kariya ga abokan huldarmu da kiyaye musu kudadensu. Wannan tsarin tantancewar zai taimaka wajen cigaba da kiyaye tsarin hada-hadar kudade ga kowa da kowa.
“Don haka muna kira ga kwastomominmu da har zuwa yanzu ba su shigar da lambobin tantancewar banki da shaidar kasancewa dan kasansu cikin bayanan asusun ba, su tabbatar sun yi hakan, kuma mu, za mu gudanar da aiki a kowani lokaci domin kowa ya samu shiga a dama da shi.”
Ya ce, dukkanin wasu korafe-korafe sun yi tsarin da za a magance wa masu hulda da su cikin hanzari kuma cikin kankanin lokaci.
Yadda Wasu Mutane Suka Ceci Junanta Ta Kimiyya Ba Tare Da Sun Taba Haduwa Ba Sakamakon ba da gudummawar kwayoyin halitta ba tare da bayyana sunansa ba, Marius Werner ya ceci rayuwar wani likita dan Burtaniya – kuma, matashin Bajamushen ya ce, watakila hakan ma ya cece rayuwarsa, domin yin hakan ya ba shi manufa a rayuwa a lokacin da ya ke tunanin kasha kansa.
Yayin da ya ke fama da cutar kansa ta jini da ba kasafai ake samun ta ba, fatan Dr Nick Embleton kawai shi ne a yi masa dashen bargon kashi.
Kuma da aka kasa samun wanda zai iya ba shi a Burtaniya, sai aka baza bincike a fadin duniya.
Shekara biyu bayan haka, BBC da kungiyar bayar da agaji ta Anthony Nolan sun taimaka wa ‘yan’uwan na jini’ wurin ganawa da juna a karon farko.
Nick ya shafe fiye da shekara ashirin ya na aiki a sashen kula da jarirai na Newcastle, yana taimakawa wajen ceton dubban kananan yara marasa lafiya a duniya. Amma a 2021, sai shi ma ya bukaci kulawar likita.
Yana tafiya a cikin asibitin, ya ce “bai san abin da ke tafe ba”. Na san cewa zan iya mutuwa, don haka na yi wasiyya,” in ji shi.
“Na tattauna wannan batun da ma tata da yarana. Na yi bakin ciki saboda yarana – ba na son su girma tsawon rayuwarsu ba tare da mahaifinsu ba.”
Dashen na sauya kwayoyin jinin da suka lalace da masu lafiya, amma jiki ya kan ki su kai tsaye sai dai idan an sami wadanda suka dace.
Charlotte Hughes, daga kungiyar ba da agaji ta Anthony Nolan, ta ce: “Mun fara bincika rajistar Burtaniya kuma muna fatan samun wanda ya dace a nan. Idan ba mu iya samu ba, to Anthony Nolan zai bincika a duk duniya don nemo wanda zai dace. Ana iya samun dace daga ko’ina.”
Da mai bayarwa da mai jinyar dole ne su kasance ba a san sunansu ba har sai an san cewa an yi nasarn dashen.
Da ya fahimci hakan, bayan shekara biyu, Nick ya shaida cewa yana son gano wanda ya ba shi gudummawar.
An gano Marius, mai shekaru 24, daga Chemniz, kusa da birnin Dresden, wanda ke cikin rajistar masu ba da gudummawa tun yana matashi. Kuma ya amince ya tashi zuwa Birtaniya ya gana da Nick, a cibiyar tallafa wa masu fama da cutar kansa ta Maggie a Newcastle, a asibitin Freeman, inda aka yi aikin dashen.
Yayin da mutanen biyu suka rungume, Marius ya ce: “Na yi matukar damuwa – ina karkarwa.”
Nick ya fada masa: “Kwayoyin cutar kansar duk sun watse. Lokacin da suka duba jinina, duk wadannan kwayoyin jinin na ka ne. Ba don kai ba da na mutu Ina da yara hudu, da sun rasa mahaifinsu. Abin da na ke son in ce shi ne, Na gode.”
Ya rasa abin fada, Marius ya yi kokarin cewa: “Ba damuwa.” Yayin da hawaye ke kwarara a fuskokinsu, Nick ya rada masa: “Na gode sosai.”