Amira Sule Matashiyar Marubuciya ce da ta rubuta Littafai masu yawa wacce sunanta ya shahara a Duniyar Marubuta, haka zalika ita ce ta yi nasarar zuwa ta daya a Gasar Hikayata ta bana, da Sashin Hausa na BBC suke shiryawa, da sauran bayanai da zaku ji daga gare ta.
A lokacin da Sani Tahir ya zanta da ita.
- Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabin Sabuwar Shekara Ga Majalissar CPPCC
- Sabon Matsayin Da Nijeriya Ta Koma A Jadawalin FIFA
Masu karatu za su so jin sanin dawa muke tare da kuma takaitaccen tarihinki?
Sunana Amira Sule Salihu, an haifeni a shekarar,16/9/1998.A cikin Garin Maradi Kasar Niger, idan na lissafa daidai shekaru na ashirin da hudu kenan a Duniya, na yi karatun addini da na Boko dukka a cikin garin Maradi,inda a halin yanzu ina koyarwa a karkashin Gwamnati a firamare (Primary), na yi aure a 2015, amma auren ya mutu, bani da yaro ko daya.
Idan na fahimce ki baki da Aure kenan a yanzu?
Gaskiya babu aure a halin yanzu
Ya aka yi kika samu kanki a harkar Rubutu?
Kafin na kasance a matsayin Marubuciya bantaba sha’awar rubutu ba, saboda kallon kebantattun mutane nake yi wa Marubuta da ba kowa ne zai iya zama ba. Kwatsam a bisa shawarar kawata, muka fara Rubuta wani labari,a nan na fahimci Marubuci ba yin sa ake yi ba,da baiwarsa ake haifarsa,kuma nima ina da baiwar.
Kin taba Rubuta Littafi ne?
Na Rubuta da dama sai dai a yanar Gizo (online) nake sakin su.
Baki buga su zuwa ga kasuwa ba kenan,shin kina da burin bugawa zuwa ga kasuwa nan gaba?
Ina kan hanyar bugawa insha Allah, nan bada jimawa ba zan sakesu a kasuwa.
Ya sunan Littafin da kika Rubuta,wane irin Labari ne?
Wanne daga ciki saboda na Rubuta littafai masu yawa bamu sunayen wasu daga ciki
Mayaudarin Masoyi, Naga Rayuwa, Ashe duk haka suke, Abdurrahim, Rawar Yan’mata, Ma’aurata, Kuskuren da na yi, Matata (mu biyu muka rubuta), Matar farko, kukan zuci, (Amma ban kammala shi ba,da matar farko).Sai wanda nake son fitarwa a kasuwa, Kallo ya koma sama,
Suma a iya Kafar yanar Gizo (online) kika rubuta ko kina da shirin fitarwa da su kasuwa domin masu karatu?
Kallo ya koma sama shi ne koda na fara Rubutawa ina da Shirin burin bugawa.Matar farko kuwa akwai wata manhaja da suke son shi, dana kammala zan sayar musu. idan dai zan buga wani daga cikin su, sai dai kukan zucin. Don sauran na rasa su, sakamakon a yanar gizo nake sakinsu, Sauya wayoyi da na ke yi yasa na rasa wasu daga ciki,
Wanne ki ka fi,so a cikin Littafan na ki?
A raina na fi son kukan zuci.
A matsayinki na Malamar Makaranta ya ya kike hada koyarwa da rubutu?
Akwai matukar wahala,ka tabo abunda yafi bani wahala,kowanne yana shiga cikin kowanne,kuma kowanne na cajin kwakwalwa ne, wannan ya sa nake fama da yawan ciwon kai a mafiyawan lokuta,wani lokacin harkar koyarwa na shiga cikin lokacin yin rubutuna, wani lokacin kuma lokacin rubutun ya shiga cikin lokacin koyarwa.
A cikin Marubuta Maza ko Mata,salon wane Marubuci ko Marubuciya ne ya ke burgeki,har ki ke koyi da halinsu,a matsayinki na Marubuciya?
Maryam Umar ita ce gwanata da kuma salonta nake yin koyi, sai Malam Hafiz Koza su biyun nan, su ne Malamai na a bangaren Rubutu na,da duk sauran Marubuta yan’uwana ababen koyi ne gare ni, matukar suka zo da abu mai kyau da ya burgeni ina dauka.
Tunda kika fara Rubutu,wane kalubale kika taba fuskanta wanda ba zaki taba mantawa da shi ba?
Gaskiya babu wani babban kalubale da zan ce ya tsayamin a rai da har ba zan mantaba. Dan abunda ya zomin da matsala da farko shi ne rashin iya daidaitacciyar Hausa, shi ma kuma sannu sannu da taimakon wadancan guda biyun,an samu canji, duk da ana koya min har yanzu. Amma wani babban kalubale kam babu shi.
Ya batun alakarki da Marubuta a Nijeriya da Nijar?
Alhamdulillah,sai sam barka, rayuwa mai matukar dadi, hadin kai karamci tare, aminci, idan abin dadi yazo ko sabanin, hakan ka, kan kasa, ga ne takamaimai waye abun ya sama,a Gaskiya banga mutane masu karamcin Marubuta ba,tsakanina da su sai dai Allah ya bar kauna.
Ya kike kallon sakon da kike isarwa ta hanyar Rubutu kina ganin yana yin tasiri a cikin Al’umma?
Masana Larabci sun ce, mafi alkairin zance shi ne wanda ya yi karanci kuma ya ba da ma’ana, Alhamdulillah yana tasirantuwa kam, da na yi rubutu mutane suna biyo ni sun samu wata mafita ko abin dauka a cikin rubutun ka ga kuwa koda mutum daya ne, ya karu ai na amfana, balle anfi haka.
Lokacin da kika shiga Gasar BBC Hausa ta Hikayata, daman kinsan ana shirya Gasar ne,ko wasu ne suka gaya miki?
Daman nasan da Gasar don ina ji a Rediyo,sai dai ban yi yungurin shiga ba,a wancan lokacin sai Bara,na fara shiga.
A lokacin da kika samu labarin kin yi Nasara a Gasar Hikayata ya kika ji, kin yi tunanin daman zaki yi Nasara?
Na yi tunanin zan yi Nasara mana, saboda kwadayin rai ga son abunda yake so,duk da na kasance cikin fargaba da razani tun bayan da aka sanar da ni, ina cikin 25, saboda gudun kar labarina, ya tsaya a iya na 12, ka chanchanci yabo, kamar bara, koma ya kasa haurawa matakin gaba, kwatsam sai na samu kira daga (BBC)a ranar wata Alhamis da ta shiga cikin kundin tarihin rayuwata.
Maganar jin dadi da farin ciki ba zai iya faduwa ba, saboda ba zan iya tantance abubuwan da na ji ba, Alhamdulillah.
A lokacin da kika koma kasar ku, kin samu tarba daga, jami’an Gwamnati da sauran al’umma ya kika kasance duba da ba kowa ake yiwa irin wannan tarba din ba?
Wallahi ba zai misaltu ba, yadda na ga motoci gaba da baya, duk don ni,na shiga wani yanayi mai wahalar fassarawa,a ya yin da manyan kasar mu,ciki harda Gwamna, da suka doso ni da sunan tarba, na yi kukan farin ciki,da murna, na ji kaina kamar wata sarauniya, saboda yadda suka karramani Allah ya saka mu su da Al’kairi sun mini ba za ta,ba zan taba mantawa da su ba.
Wacce shawara zaki bawa Marubuta da sauran jama’ar Gari?
Su nemi ilimi a duk abun da suka, saka a gaba su yi aiki mai nagarta da kwadayin kawo taimako cikin al’umma, ba don neman daukaka ba. Domin ita daukaka ba gayyatota ake ba,zuwa take da kanta,nagarta aiki tukuru da tsananin sa’a kan kawo ta.
Da wannan ne koda mutum ya bar Duniya za su zama ababen Bege,da kauna alfahari,kuma ayyukansu zazu cigaba da wanzuwa saboda irin kyawawan Aikin da suka yi.
Ina Godiya ga daukacin Yan’uwa da abokan arziki akan sahihiyar kauna da suke nunamin dangane da wannan nasara da na samu,hakika na kara tabbatarwa mutum Rahama ne,ba abunda da zance da masoya sai Allah ya saka da kyakkyawan sakamako,ya bar kauna,ina alfahari da masoya,ina musu kyakkyawar kauna tun daga kasan raina.
Ko kina da wani karin bayani wanda bamu tambayeki ba?
Bani da wani karin bayani
Muna Godiya
Nima Na gode kwarai da gaske