Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq a ranar Alhamis ya sanar da bayar da Naira miliyan 100 a matsayin tallafi ga wadanda hatsarin kwale-kwale ya rutsa da su a baya-bayan nan da mutane kusan 200 daga karamar hukumar Kaiama ta jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai wa Mai Martaba Sarkin Kaiama, Alh. Umar Mu’azu Kiyaru IV inda ya jajantawa Sarkin da al’ummar garin Kaiama.
- Majalisa Ta Amince Jami’an Kiyaye Haɗurra Su Riƙe Bindiga
- Kotu Ta Sake Dakatar Da Sarki Ado Daga Gyara Fadar Nassarawa
Ya kuma mika sakon ta’aziyyar shugaban kasa Bola Tinubu ga sarkin da kuma al’ummar garin Kaiama, inda ya ce tawagar shugaban kasa ba ta iya zuwa jihar Kwara a ranar Alhamis ba saboda rashin kyawun sararin samaniya da ke ba jiragen sama damar sauka da tashi.
Sarkin Kaiama ya yabawa gwamnan bisa ziyarar tun da farko da ya aike da tawaga mai karfi karkashin jagorancin kakakin majalisar dokokin jihar Kwara, Engr. Yakubu Danladi-Salihu ga al’ummar da abin ya shafa.
Sarkin ya ce, duk da cewa, lamarin wani abu ne na Allah, domin kuwa babu wani rai da zai mutu ba tare da saninsa ba, amma yana da kyau mutane su mutunta ka’idojin kiyaye lafiya kamar amfani da rigunan kare rai da guje wa wuce gona da iri da tafiyar dare.
Ya godewa gwamnan bisa wannan gudummawar da kuma goyon bayan da yake bai wa jama’a a koda yaushe.