Mataimakiya ta musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal kan harkokin Ilimin mata, Hajiya Aishat Maina ta rasu.
Ta rasu ne bayan halartar taron gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da ya gudana a Jihar Sakkwato a ranar Talata.
- Sin Na Tsayawa Tsayin Daka Kan Yaki Da Ta’addanci
- Da Dumi-Dumi: Mahara Sun Kashe DPO Da Wasu A Benue
Leadership Hausa ta gano cewa, ta shiga cikin turmutsitsin da ya afku a kofar fitta daga filin taron.
“Wani direban babur ne ya fado daga kan babur dinsa a hanyar fita dava filin wanda hakan ya haifar da mumunan turmutsutsu, inda mutane suka fado kan juna. Tana daya daga cikin wadanda abin ya shafa,” cewar wata majiya.
Da yake tabbatar da hakan, shugaban kungiyar masu ba da shawara na musamman, Ibrahim Magaji Gusau, ya ce an ceto marigayiyar, inda aka garzaya da ita Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato domin yi mata magani.
“Abun takaici ta mutu ‘yan mintuna kadan bayan kai ta asibiti,” in ji shi Magaji, wanda ya bayyana ta a matsayin mai kwazo da hazaka.
“Ko a lokacin taron, muna tare, ba tare da sanin cewa hakan zai zama taronmu na karshe ba,” in ji shi, ya yi mata addu’ar Allah ya gafarta mata kurakuranta, ya kuma sanya ta a Jannatul Firdaus.
Marigayiyar dai tsohuwar shugabar kungiyar ‘yan jarida ce ta kasa (NAWOJ) a Jihar Sakkwato.
Ta kuma kasance tsohuwar mai bai wa Gwamna Aminu Tambuwal shawara kan sabbin kafafen yada labarai kafin a dauke ta zuwa Hukumar Ilimi ta Mata.
Tsohon Shugaban Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ) a Jihar Sakkwato, Isa Abubakar Shuni, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar ‘yar jaridar ba zato ba tsammani, inda ya bayyana cewa ta ba da gudunmawa sosai ga harkar aikin jarida a jihar.
Ta rasu ta bar ‘ya’ya uku da kuma iyayenta tsofaffi.