Assalamu alaikum masu bibiyarmu a wannan shafin namu mai tarin farin jini da albarka na Girki Adon Mata. To a yau ma mun zo muku da sabon salon a abinci mai kayatarwa shi ne, wani hadadden abin Karin kumallo
Abubuwan da Uwargida za ta bukata:
Filantan, kwai, mai, tattasai, tumatur, albasa mai lawashi, magi da gishiri, kayan kamshi, tanda ta suyar masa.
Da farko za ki samu filantan dinki mai kyau wadda ba ta lagube ba sabuwar diba, sai bare bawon, sannan ki raba ta biyu a kwance sannan ki dauki daya ki yanka ta a tsaye sannan ki sake yanka daya gefan kin ga yankan ya zama gida hudu kenan, sannan ki yayyanka ta a kwance kanana, haka za ki yi har ki gama kowacce kika dauka haka za ki mata har ki gama yayyanka su gaba daya.
Daga nan ki zuba mai a abin suya ki dora shi a wuta ki sa masa ‘yar albasa saboda ya yi kamshi, idan man ya yi sai ki zuba wannan yankakkiyar filantan din, ki soya ta kamar yadda ake soya filantan ta yi kamar ruwan kasa, sannan ki kwashe ta sai ki samu wata roba ki fasa kwai kamar daidai yadda zai ishe ki ki kada shi, sannan ki zuba wannan filantan din da kika soya sai ki zuba tattasai wanda dama ki gyara shi kin jajjaga shi, sannan ki zuba tumatur, amma shi yayyanka shi za ki kanana, sannan ki yanka albasa tare da lawashinta ki zuba sai ki zuba magi da gishiri da kayan kamshi ki juya su sosai kamar za ki yi wainar kwai ko kuma masa, sannan sai ki dora tandarki a wuta idan so samu ne ki samu sabuwar fitowannan wadda ba ta makera ba tafi kyau gaskiya.
Sannan ki dan zuzzuba mai kamar za ki soya waina idan man ya yi zafi sai ki debo wannan hadin filantan din kina zubawa a kowanne gida amma ki rage mata wuta saboda ta gasu a hankali don cikin shima ya gasu, idan kasan ya gasu za ki ga ya yi kamar kwai sai ki juya ta saman ma ya gasu, idan ko’ina ya gasu ki tabbatar kin duba cikin shima ya gasu haka za ki yi har ki gama, za ki ga ya yi abin akwai burgewa.