Daya daga cikin dattawa a masana’antar Kannywood wadanda su ka shafe shekaru fiye da 30 a Kannywood ana damawa dasu a mabanbantan ayyuka, kamar shiryawa, daukar nauyi, rubuta labari da kuma fitowa a matsayin jarumi Ado Ahmed Gidan Dabino kuma Sarkin Mawallafan Arewacin Nijeriya, ya bayyana batutuwa da dama dangane da wannan masana’antar ta nishadi da ke Arewacin Nijeriya.
A wata hira da ya yi da Radio France International Gidan Dabino wanda ya lashe kyaututtuka da dama a ciki da wajen Nijeriya a matsayin jarumi ko wani rukuni na shirin fim, ya ce masana’antar fina-finan kudancin kasar sun ci gaba a wasu bangarori fiye da takwararta ta Arewacin Nijeriya.
- Nijeriya Ta Yi Asarar Tiriliyoyin Naira Kan Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba – Gwamnati
- NNPC Da Matatar Dangote Na Gasar Rage Farashin Fetur
Haifaffen Dawakin Kudu da ke Jihar Kano, Gidan Dabino ya yi karantunsa a makarantun Allo da na Islamiya kafin ya shiga makarantar ilimin manya, daga nan ya wuce sakandiren gwamnati a Gwale wadda itama ta ke karkashin hukumar da ke kula da ilimin manya, Ado ya zarce Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya samu shaidar matakin Diploma a bangaren ‘Mass Communication’.
Da yake amsa tambaya a kan yadda ya tsinci kanshi a masana’antar Kannywood ko kuma wasan kwaikwayo, jarumin ya ce tun a shekarar 1984 yake wannan harka kafin kafa masana’antar Kannywood inda a wancan lokacin suke yin wasannin kwaikwayo na dabe kafin zuwan Talabijin.
Dangane da kalubalen da Kannywood ke fuskanta, Ado Ahmed ya ce wannan ba komai ba ne illa zuwan zamani domin kuwa yanzu komai ya koma kan yanar gizo ba kamar a lokacin baya ba, yanzu abubuwa sun canza domin yanzu idan ka shirya fim sai dai kaje ka dora abinka a shafukan yanar gizo kamar YouTube da sauransu, ko kuma ka samu wani gidan Talabijin ya saye fim fim din daga hannunka.
Hakan ya sa yanzu ba kasafai masu shirya fina finan Hausa ke mayar da adadin abinda su ka kashe wajen shirya fim ba, don kuwa ba kowane yake da yawan mabiyan da za su kalli abinda ya dora a YouTube ba da har zai samu wani abin kirki, hakazalika gidajen Talabijin da ke saye ba wani kudin azo a gani suka bayarwa ba, yanzu idan fim dinka bai kai matsayin shiga tashar NETFLID ta kasar Amurka ba, ba lallai ne ya kai inda kake bukata ba inji shi.
Ya ci gaba da cewa hakan yasa nike bayar da shawara wajen ganin mun fadada tunaninmu wajen zakulo wasu sabbin hanyoyi da zamu dinga fitar da fina finanmu zuwa inda ya kamata domin samun kudaden shiga kamar sauran abokan sana’armu da ke Kudancin Nijeriya, inda zaka ji sun samu miliyoyin kudade ta hanyar fina finansu.
Sannan kuma akwai bukatar hadin kai a tsakaninmu ta yadda zamu kasance tsintsiya madaurinki daya, misali idan mutum daya zai iya zuba jarin miliyan 10 ya shirya fim din da ba zai iya zuwa koina ba, kamata ya yi ace mutane da yawa sun hadu sun zuba jari mai yawa wajen shirya fim din da zai iya tasiri a idon Duniya kuma su samu manyan kudaden da za su cire kudin da su ka zuba su kuma samu kudaden da za su shirya wani fim din a gaba.
Daga karshe Ado Ahmed Gidan Dabino ya bukaci jaruman fim, wadanda su ka samu wani mukami na jagoranci a masana’antar ko kuma a cikin gwamnatin jiha ko ta tarayya, da su dinga kwatanta adalci bakin gwargwado kuma su dinga tunawa da abokan sana’arsu wadanda ba su samu irin wannan damar ba yayin gudanar da mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp