Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan makon cikin shirinmu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
A yau shafin na mu zai koya muku yadda ake hada Lemon Tsamiya
Abubuwan da za ku tanada:
Tsamiya, citta danya, Suga, filebo:
Ga kuma yadda za ku hada:
Da farko za ku wanke tsamiya sai ku dafa ta ku tace ta, sannan ku wanke danyar citta, sai ku nikata ku samu roba mai kyau ku tace tsamiyar tare da cittar ku sanya suga da filebo sai ku juya sosai ku sanya a firij ko ku sanya masa kankara. Asha dadi lafiya.
Hade-haden Lemon Shayi:
Abubuwan da za ku tanada:
Kankana, Kwakwamba, Sitoru Beri Na Ruwa, Lemo, Tea Bag, Danyar Citta, Abarba, Lemon Juice, Na’a na’a:
Yadda za ku hada:
Da farko za ku wanke kankana da danyar citta sai ku nika su sannan ku tace ku zuba a cikin tukunya sai ku dora akan wuta sannan ku wanke abarba da kwkwamba sai ku yanka ku zuba a cikin tukunya ku sa tea bag dinku a ciki idan ya tafasa sai ku sauke sannan ku wanke lemo sai ku matse a wata roba za ku sami roba me kyau sai ku tace lemon da kuka matse da hade-haden lemon shayin a ciki, sai ku sa Sitoruberi na