Assalamu alaikum. Barkammu da sake saduwa a wannan makon a cikin shirin namu na Girki Adon Mata, za mu yi bayani kan yadda za ki yi hada lemo kala-kala na ‘ya’yan Itatuwa:
Lemon Kokumba Da Tuffa: Abubuwan hadawa Kokumba, Tuffa, Madara, Suga, Flavour.
Yadda A Ke Hadawa
Da farko za ki wanke kokumbar da tuffa sai ki yanka su kanana ki zuba a blender ki markada, sai ki tace ki zuba madara da suga da flabour sai ki juya shi sosai, sannan ki juye shi a jug ki sa kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi. A sha dadi lafiya.
Lemon Na’a Na’a
Abubuwan hadawa: Ganyen na’a na’a ( mint leabes) Tsamiya, Suga, Filebo ( flabour).
Da farko za ki wanke tsamiyarki ki dora a wuta ki tafasa sai ki wanke ganyen na’a na’arki ki yi markada shi sannan ki duba tsamiyarki idan ta tafasa sai ki sauke ki tace idan kin tace sai ki tace na’a na’a ki hade su wuri guda ki zuba suga da filebo sannan ki sa a cikin firij ya yi sanyi.
Lemon Mangwaro
Kayan hadi; Mangwaro, Suga, Flabour, Lemon tsami.
Da farko za ki sami mangwaronki irin manyan nan ki wanke ki fere, bayan haka ki yanka ki zuba a blanda sai ki matse lemon tsaminki a wani abu ki tace shi ma mangwaron ki tace ki hada su waje daya ki zuba suga da filebo, sannan ki juya sosai ki dandana idan ya yi sai ki sa kankara ko ki sa afirji ya yi sanyi.
A sha dadi lafiya