A wannan makon ma za mu ci gaba da kawo muku tattaunawar da muka yi masu kananan sana’o’I don sanin halin dasuke ciki bayan cire tallafin man fetur da aka yi.
Ya sunan Malamin?
Sunana Mallam Zaiyanu
Mece ce sana’arka?
Ina tuki ne daga Zuba zuwa cikin gari kuma in Juyo
Mallam Zaiyanu shin wane hali kake fuskanta dalilin wannan canjin yanayi da muke ciki?
Mu direbobi muna fuskantar matsaloli da yawa don yanzu ga motocin ma amma ba mutane saboda halin da muke ciki ga tsadar rayuwa komai ya kara kudi, kudin mota ya karu fasinjoji sai korafi suke yi, gani suke kamar mu muka yi karin wani ma sai ka sauke shi idan ka karbi kudi ya ce canjin shi bai cika ba.
Ya yanayin sana’ar take a da?
A da lamarin akwai dan sauki duk da dai da din ma ana korafin amma na yanzu ya fi yawa ga gyaran mota da za a yi kuma sai ka duba idan ba ka kai zuciya nesa ba gaskiya za ka daina sana’ar, man da da ake cika tanki yanzu kudin da kake saya da shi za ka samu rabin tanki gaskiya ana cikin tsadar rayuwa.
Wasu ma ajiye motar kawai suka yi saboda tsanani. maaikata ma sun rage shiga cikin gari duk karin albashin da aka yi kudin duk na tafiya a kudin mota.
Wane kira za ka yi wa gwamnati?
Ina kira da babbar murya da su yi wani abu akai