Jirgi na farko dauke da mahajjata 425 na birnin tarayya Abuja da suka gudanar da aikin hajjin bana a kasar Saudiyya, ya sauka a birnin Abuja lafiya.
Da take tabbatar da isowar jirgin, hukumar ta tabbatarwa da iyalai da ‘yan uwa na sauran mahajjatan cewa, ana kokarin ganin an dawo da sauran maniyyatan dukkansu cikin kwanciyar hankali a kan lokaci a cikin kwanaki masu zuwa.
ADVERTISEMENT
- Abba Ya Dace Ya Zama Gwamnan Kano Na Har Abada Ba Shekaru 8 Kaɗai Ba – Arch Ali Hassan
- Barayin Wayar Lantarki Sun Addabi A’lummar Jihar Kebbi
A cewar jami’an, ana sa ran, yau Litinin 23 ga watan Yuni, jirgi na biyu dauke da mahajjatan zai iso gida Nijeriya.
Hukumar ta kuma jaddada cewa, ana kokarin ganin an kawar da duk wata barazana domin dakile duk wani jinkirin da bai kamata ba.














