Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta ce kowane maniyyaci da zai je aikin Hajjin 2003, zai biya Naira miliyan 2.89.
Shugaban hukumar na kasa, Zikrullah Hassan ne, ya sanar da hakan a yau Juma’a, inda ya danganta hakan da hauhawar farashin kaya a Nijeriya da kuma Saudiyya.
- An Samu Tsohuwar Hedimasta Da Laifin Yi Wa Dalibai Fyade
- Buhari Ya Gaza Gudanar Da Sahihin Zabe A 2023 – Kwankwaso
Hassan, ya ce an tsara farashin bisa kashi takwas, inda jihohin Borno da Yobe, ke da karancin farashi sai kuma jihohin Legas da Ogun na su farashin ya fi yawa, wanda ya kai Naira miliyan 2.99.
Rahotannin sun bayyana cewa, karin kudin hajjin ya kai sama da Naira 300,000, inda aka kwatanta da kudin da alhasai suka biya a 2022.
Ya kara da cewa, farashin aikin hajjin, tsadarsa kashi takwas ne, inda maniyyacin da ya fito daga Maiduguri da wanda ya fito daga Yola, kowanensu zai biya Naira miliyan 2.89 sauran wadanda suka fito daga jihohin Arewa kuwa, kowane maniyyaci zai biya Naira miliyan 2.919.
A cewarsa, kudancin kasar kuwa, na da farashin kashi shida, inda Jihar Edo da sauran jihohin da ke a Kudu maso Kudu da kuma a Kudu maso Gabas kowane maniyyaci zai biya Naira miliyan 2.9, inda kuma wadanda suka fito daga jihohin Ekiti da Ondo, kowane zai biya Naira miliyan 2.88.
Kazalika, ya ce kowane maniyyaci daya da ya fito daga Jihar Osun, zai biya Naira miliyan 2.99, inda maniyyaci daya da ya fito daga Jihar Kuros Ribas zai biya Naira miliyan 2.943, haka kowane maniyyacin daya da ya fito daga jihar Legas, Ogun da Oyo, zai biya Naira miliyan 2.99.
Ya ce an samu bambamcin farashin ne domin jihohin da ke Arewa sun fi makwabtaka da Saudiyya fiye da sauran jihohin da ke a kudancin kasar nan, inda kuma masaukan maniyyatan da kowace jiha za ta kama ke nuna abin da ya kamata maniyyaci zai biya.
Bugu da kari, kamfanonin jiragen saman da aka sahale wa su yi jigilar maniyyatan zuwa kasar mai tsarki su ne; Air Peace, Azman Air, Fly Nas, Aero Contractors da kuma Max Air, inda Arik Air da kuma Value jet.
Shugaban, ya ce za rufe rumbun adana bayanan hukumar ga wadanda suka yi zabi su shiga shirin zuwa kasar mai tsarki ta hanyar zuba kudin adashin gata a ranar 21 ga watan Afirilu, 2023.