ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Samu Tsohuwar Hedimasta Da Laifin Yi Wa Dalibai Fyade

by Sabo Ahmad
3 years ago
Fyade

An samu wata tsohuwar shugabar makaranta, ‘yar asalin Isra’ila da laifin cin zarafin wasu dalibanta biyu a wata makarantar Yahudawa da ke Australia.

Kotu a birnin Melbourne na Australia ta samu Malka Leifer da laifin cin zarafin wasu yara mata guda biyu Dassi Erlich da Elly Sapper tsakanin shekarun 2003 zuwa 2007.
Sai dai, ba a same ta da laifin yin lalata da yarinya ta uku da aka tuhume ta a kai ba, Nicole Meyer.

  • Yadda Tsarin Demokuradiyya Ya Samu Cikakkiyar Daraja A Kasar Sin

Leifer, mai shekara 56 ta musanta zarge-zargen da aka yi mata tun da farko, kuma ta kwashe shekaru tana kokarin ganin ba a mayar da ita Australia daga Isra’ila ba.

ADVERTISEMENT

Sai dai a 2021 ne kotu ta ba da umurnin mayar da ita Australia din daga Isra’ila.
Daliban sun ce Leifer ta yi lalata da su a cikin aji, da kuma lokutan da suka kai ziyara gidanta daga makaranta.

Mai gabatar da kara Justin Lewis ya ce Leifer ta bayyana alamun cewa ita mai son bin mata ce.

LABARAI MASU NASABA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

Ya ce ta yi amfani da matsayinta da kuma kuruciyar yaran da rashin saninsu game da abubuwan da suka shafi saduwa wajen ganin ta cimma nufinta.

Yaran a wancan lokacin ba su san komai game da lalata ba, saboda irin tarbiyyar da aka ba su, inda aka hore su kan tsarin rayuwa ta tsantsar bin addinin Yahudu. In ji mai gabatar da karar.

Ya kara da cewa “Kasancewar ta san an yi watsi da su a gida, sai ta nuna tamkar tana son su, kuma ta ce musu tana taimakon su ne.”

Sai dai lauyan wadda ake zargi, Ian Hill ya ce zarge-zargen ba su da tushe.
Ayarin masu kare ta din sun ce ba ta samu damar kare kanta yadda ya kamata ba, saboda tsawon lokaci bayan faruwar lamarin.

Leifer ta tsere zuwa Isra’ila bayan da aka tayar da maganar zarge-zargen.
Sai dai an kama ta a 2014 bayan da Australia ta bukaci hakan, amma shekara biyu da ta wuce, sai wata kotun Isra’ila ta soke batun mayar da ita Australia, inda kotun ta ce tana da tabin hankali.

Amma masu bincike na farin kaya sun dauko hotunanta tana sayen kaya a kanti da kuma ajiye kudi a banki, abin da ya sanya Isra’ilar ta sake kama ta tare da gurfanar da ita a kotu cikin watan Fabrairun 2018.

Sannan bayan kwashe mako biyu ana sauraron karar an samu Leifer da laifi 18 wadanda suka jibanci cin zarafin Ms Erlich da Ms Sapper.

Za a yanke wa Leifer hukunci nan gaba kadan.

Fyade
Sabo Ahmad
+ postsBio
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    An Gurfanar Da Mutum 3 Bisa Laifin Lakada Wa Wani Duka Har Lahira
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Tasa Keyar Dakta Idris Dutsen Tanshi Zuwa Gidan Yari
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    Uwa Ta Mutu A Kokarin Raba Fada Tsakanin ‘Ya’yanta A Abuja
  • Sabo Ahmad
    https://hausa.leadership.ng/author/sabo-ahmad/
    ’Yan Fashi Sun Yi Shigar Injiniyoyi, Sun Saci Manyan Na’urorin Sadarwa

MASU ALAKA

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota
Kotu Da Ɗansanda

Direbobi 123 A Kano Suna Fuskantar Tuhuma Kan Laifin Keta Dokokin Amfani Da Lambar Mota

July 18, 2026
An Kama Matashi A Kano Kan Zargin Kashe Abokinsa
Kotu Da Ɗansanda

‘Yansanda Sun Kama Mutum Biyu Kan Zargin Damfarar Wayar Salula A Jihar Adamawa

July 18, 2026
Disu
Kotu Da Ɗansanda

IGP Disu Ya Hana Jami’an Ƴansanda Yin Amfani Da TikTok Da Instagram Da Sauransu

June 26, 2026
Next Post
Goro

GORON JUMA’A

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.