Kwanaki uku da fara jigilar maniyyata aikin Hajji na shekarar 2023 a Nijeriya, hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kwashe alhazai 2,996 zuwa kasar Saudiyya.
Idan baku manta ba, Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya samu wakilcin Karamin Ministan Harkokin Waje, Amb. Zubairu Dada, a ranar Alhamis, 25 ga watan Mayu, 2023, inda ya kaddamar da aikin jigilar jiragen sama na shekarar 2023 a tashar Alhazai ta filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja tare da alhazai 472 daga jihar Nasarawa da jami’an NAHCON 27 a cikin jirgin farko na Max Air zuwa Madina.
- Hukumar Aikin Hajji Ta Warware Sarkakiyar Karin Kudi Ga Maniyyata
- NAHCON Ta Nemi Alhazai Su Biya Kashi 40 Na Dala 250 Na Jigilarsu
Wani sabon rahoto da hukumar NAHCON ta fitar ya nuna cewa a ranar Juma’a 26 ga watan Mayu kashi na biyu na alhazai ya tashi daga jihar Bauchi a jirgin MaxAir mai lamba NGL1001 zuwa Jeddah tare da alhazai 549 daga jihar Filato, wadanda suka kunshi maza 339 da mata 210 a cikin jirgin.
Haka kuma a ranar Juma’a jirgin NIG9005 ero Contractor ya tashi daga Abuja zuwa Madina, inda ya yi jigilar maniyyata 450 daga jihar Nasarawa da jami’ai 13. Mahajjatan da ke cikin jirgin Aero Contractor inda yake dauke da maza 275 da mata 175. Wannan dai shi ne karo na uku da aka yi jigilar Alhazai, ya kai jimillar Alhazai 1,471.
Asabar da ta gabata an yi jigalar Alhazai zuwa Madina tare da maniyata 841 da 422 na jihohin Sokoto da Zamfara, yayin da Air Peace. Jirgin mai lamba P47902 ya taso daga Legas zuwa Madina tare da mahajjata 262 daga jihar Kwara, wanda ya kawo adadin maniyyatan da aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya ya zuwa yanzu jimilla 2,574.
An yi jigilar mahajjatan zuwa kasa mai tsarki a cikin jirage biyar daga filayen tashi da saukar jiragen sama guda hudu da kuma jiragen guda hudu masu jigilar alhazai na jihohi biyar daban-daban.