Wasu daliban Jami’ar Bingham uku sun fada komar ‘yansanda kan zarginsu da kashe wani direban motar bolt da ya daukes u domin su sayo tabar wiwi a Abuja.
Kisan nasa na zuwa ne bayan rashin jituwar da ta barke a tsakaninsu kan biyansu kudin jigilarsu da ya yi.
- Halin ‘Yan Siyasa Na Ba Sarakuna Mamaki – Sarkin Zazzau
- Gwamnatin Kaduna Ta Tabbatar Da Bullar Cutar Diphtheria A Kafanchan
Kwamishinan ‘yansandan birnin tarayya (FTC), Haruna Garba, shi ne ya tabbatar da hakan wa ‘yan jarida a ranar Alhamis.
A cewarsa, ‘yansanda sun samu rahoton gano gawar mamacin, Obasi Okeke, kwance macacce cikin jininsa a Ngugu Close, Area 11, Garki, Abuja.
A fadinsa, daya daga cikin wadanda ake zargin ne ya kira mamacin domin ya daukesu zuwa yankin Guzape da ke Abuja, sannan ya kaisu ya kuma dawo da su inda ya daukesu.
Ya ce, “A ranar 5 ga watan Yunin 2023, aka samu gangar jikin wani direba mai suna Obasi Okeke, kwance macacce cikin jininsa a Ngugu Close Area 11 Garki Abuja. ‘Yansanda sun dauki gawar domin kaddamar da bincike kan makasan direban.
“Binciken wadanda suka aikata wannan danyen aikin ya kai ga cafko wasu da ake zargi masu suna Obasieyene Inemesit Inem, Aaron Anthony da Alasan Ayomide Olusegun, wadanda dalibai ne na jami’ar Bingham, biyu daga cikin su ma su na matakin dakatarwa daga jami’ar.
“Daya daga cikin su ne ya kira direban domin ya kai su inda za su sayo tabar wiwi.
“Dawowarsu daga Guzape, inda ya daukesu. Sai suka fahimci ba su da kudin da za su biyu shi tukasu da ya yi, sai suka yanke shawarar yaudararsa ta hanyar nuna masa shaidar tura kudi na karya ‘debit alert’ a wayarsu, amma sai shi direban ya kage kai da fata cewa bai samu sakon kudi ba.
“A wannan gabar da suke takaddama, daya daga cikin wadanda ake zargin ya zaro wuka ya soka wa direban sai suka arce daga wajen.”
“Kuma tunin wadanda ake zargi su ukun suka amsa laifinsu, za mu gurfanar da su a gaban kuliya ba da jimawa ba,” a cewar CP.