• English
  • Business News
Saturday, September 6, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa

by Sadiq
3 months ago
in Manyan Labarai
0
Hajjin 2025: Alhajin Kano Ya Rasu A Makka Kwana Ɗaya Kafin Arfa
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wani mahajjaci daga Jihar Kano mai suna Shu’aibu Jibrin ya rasu a birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya, kwana ɗaya kafin a fara gudanar da ibadar Hajji ta shekarar 2025.

Mai magana da yawun Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano, Malam Suleiman Dederi, ne ya tabbatar da rasuwar Jibrin, inda ya ce marigayin ya rasu a ranar Talata bayan wata gajeriyar rashin lafiya.

  • Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai
  • Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba

Ɗaya daga cikin ‘yan uwansa, Sama’uddin Aliyu Kadawa, wanda shi ma na cikin mahajjatan, ya shaida wa manema labarai a Makka cewa marigayin yana cikin ƙoshin lafiya kafin tafiyarsu daga gida.

“Bayan ya fara jin jiki, an kai shi Asibitin Sarki Abdulazeez inda ya kwana biyu kafin a sallame shi saboda ya samu lafiya.

“Amma daga baya sai yanayinsa ya ƙara taɓarɓarewa, aka sake garzayawa da shi asibiti. Duk da ƙoƙarin likitocin Nijeriya da na asibitin Saudiyya, ya rasu da misalin ƙarfe 2:50 na dare,” in ji shi.

Labarai Masu Nasaba

Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato

NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

Aliyu, ya bayyana cewa Jibrin manomi ne daga ƙauyen Gargai da ke ƙaramar hukumar Bebeji a Kano.

Ya kuma ce yana fama da cutar gyambon ciki da hawan jini.

Likitoci sun bayyana cewa rasuwarsa ta faru ne sakamakon bugun zuciya da gazawar zuciya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AlhajiHajjiMakkahRasuwa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Muhammadu Iliyasu Bashir A Matsayin Sarkin Gwandu

Next Post

Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

Related

Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato
Manyan Labarai

Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato

1 hour ago
NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai
Manyan Labarai

NUPENG Za Ta Fara Yajin Aiki, Dangote Na Shirin Shiga Harkar Sufurin Mai

8 hours ago
Mahara Sun Kai Hari Banki A Kogi
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Wasu 156 Kan Aikata Laifuka A Jigawa

23 hours ago
Sojoji Sun Kwato Makamai Da Babura, Sun Ceto Mutane 3 A Kaduna 
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kama Ɗan Bindiga Ɗauke Da Makamai A Jihar Filato

1 day ago
Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

1 day ago
Ministan Tsaro
Manyan Labarai

Dawowar Matsalar Tsaro: Ta Haifar Da Cece-kuce Kan Daukar Matakin Kare Kai

1 day ago
Next Post
Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

Hajjin Bana: Falalar Tsayuwar Arfa

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Fara Binciken Yadda Matasa Suka Kone Wata Mata Har Lahira A Neja

‘Yansanda Sun Fara Binciken Yadda Matasa Suka Kone Wata Mata Har Lahira A Neja

September 6, 2025
Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato

Mutanen Gari Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Wasu A Sakkwato

September 6, 2025
Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

Nazari Kan Bukatar Manoma Su Rika Yi Wa Mangwaro Ban-ruwa

September 6, 2025
Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

Muna Bukatar Karin Hekta 500,000 Domin Noman Kwakwar Manja – POFON

September 6, 2025
Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

Gwamnatin Kogi Ta Jaddada Aniyar Magance Ambaliya Da Zaizayar Ƙasa

September 6, 2025
Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

Zulum Ya Ba Da Tallafin ₦300,000 Ga Iyaye, Da Ciyar Da Ɗalibai 90 Kyauta A Borno

September 6, 2025
A Zango Mai Zuwa Za A Fara Aikin Dala Miliyan Daya A Tashar Jirgin Ruwa Ta Legas – Dantsoho

Kungiyoyi Da Abokan Arziki Na Ci Gaba Da Taya Dantsoho Murna

September 6, 2025
Fursunoni Ba Za Su Samu Damar Kada Kuri’a Ba A Zaben 2023 – INEC

Rudani Ya Kunno Kai Yayin Da INEC Ta Ki Amincewa Da Shugabancin ADC

September 6, 2025
Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC

Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC

September 6, 2025

Ilimi Shi Ne Matakin Nasarar Rayuwar Duniya Da Lahira – Yerima Shettima

September 6, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.