Shugaban Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh, ya sha alwashin ba zai bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ‘yan Nijeriya kun ya ba lokacin gudanar da aikin hajjin 2025.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Abdullahi Saleh, ya bayyana cewa hukumar ta himmatu wajen gudanar da ayyukanta, musamman aikin hajjin 2025.
- Matsalar Wuta Ta Jefa Wasu Sassan Nijeriya Cikin Duhu
- Masana Kimiyya Na Sin Sun Gano Tsare-Tsaren Rayuwa A Muhallin Halittu Mafi Zurfi A Teku
Ya ce an yi tanadin yadda za a yi aikin hajjin 2025 cikin kwanciyar hankali, yana mai cewa duk maniyyatan da suka yi rajista za su samu darajar kudinsu.
Shugaban hukumar ya kara da cewa tuni hukumar ta samu gagarumin ci gaba a kokarinta na inganta aikin hajji ga daukacin alhazan Nijeriya.
Abdullahi Saleh ya ce, “Ina so in tabbatar wa mai girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa NAHCON da ke karkashinsa ba za ta bar ‘yan Nijeriya su yi kasa a gwiwa ba, domin aikin hajjin 2025 zai kasance wanda ba a taba ganin irin sa ba.
“Bisa ga ajandar sabunta fata na Shugaba Tinubu, mun himmatu wajen tabbatar da manufofi da ka’idojin da suka jagoranci hukumar tsawon shekaru.
“Ina kuma tabbatar wa ‘yan Nijeriya, musamman maniyyatan da suka yi niyyar zuwa aikin hajjin 2025, za su gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da NAHCON bisa sakamakon aikin hajjin 2025.
“Shugaban kasa yana tsayawa kan Magana daya. Yana ba mu dukkan goyon bayan da ya kamata. Ba za mu ci amanarsa ba. Ba za mu sauka daga kan manufarmu ba.
“A kan wannan, dole ne mu gode wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima bisa yadda suka ba mu amanar tafiyar da harkokin aikin hajji.
“Hukumar ta samu wasu nasarorin da suka shahara a cikinsu akwai kwato sama da naira biliyan biyar na ayyukan da ba a yi wa maniyyata aikin hajjin 2023 ba, wanda ya nuna jajircewarmu na yin aiki da gaskiya da kuma kare muradun mahajjatan Nijeriya.
“Mun kuma yi aiki tare da Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya don tabbatar da bayar da fasfo na maniyyata a kan lokaci.
“A hankali a hankali muna aiwatar da wasu muhimman tsare-tsare don tabbatar da gudanar da aikin hajjin 2025 cikin kwanciyar hankali, musamman dangane da samar da ayyukan jin dadin maniyyatanmu.”
Sai dai Farfesa Abdullahi Sale ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da mara wa ayyukan hukumar baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp