Yayin Da Obasa Ya Dawo, Mernda Ta Yi Murabus Bayan cece-kuce a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki da kan rikicin shugabancin da ya turnike a majalisar dokokin Jihar Legas, Honorabul Mudashiru Obasa ya sake dawowa kan kujerarsa na shugabancin majalisar dokokin Jihar Legas.
Maido da shi cikin kan kurerar ya bayar da mamaki, bayan da Honorabul Mojisola Meranda ta yi murabus tare da komawa matsayinta na mataimakiyar shugabar majalisar, shi ne ya dau hankalin ‘yan Nijeriya wanda suka zuba ido su ga yadda abubuwan za su kasance a wannan zauren majalisa.
- Matsalar Wuta Ta Jefa Wasu Sassan Nijeriya Cikin Duhu
- Masana Kimiyya Na Sin Sun Gano Tsare-Tsaren Rayuwa A Muhallin Halittu Mafi Zurfi A Teku
Yanzu dai idanuwa sun karkata ga Obasa a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke dakon ganin mataki na gaba na aiwatar da yarjejeniyar, yayin da rahotanni suka ce ana bukatar ya yi murabus daga ofis domin samar da hanyar da za a bi wajen ganin dan takara mai sassaucin ra’ayi ya fito a matsayin sabon shugaban majalisar.
Majiyoyin sun shaida cewa, ya kamata a fito da sabon shugaban majalisar dokokin Legas nan da sa’o’i 48 masu zuwa, bisa yarjejeniyar da aka kulla da ta share fagen sauye-sauyen shugabanci da aka yi a ranar Litinin.
Rikicin shugabancin da ya dabaibaye majalisar dokokin Jihar Legas ya mayar da hannun agogon ‘yan majalisar jihar baya.
Rikicin ya fara ne tun bayan tsige Obasa a ranar 13 ga Janairu, 2025, a matsayin shugaban majalisar. ‘Yan majalisa 33 a zaman da aka yi a wannan rana suka tsige Obasa tare da ayyana tsohowar mataimakiyar shugaban majalisar, Merand a matsayin shugaban majalisar dokokin Jihar Legas.
Ko da yake ’yan majalisar sun yi nuni da cewa yana cin zarafin mukami da karkatar da kudade da kuma rashin da’a a matsayin wani bangare na dalilan tsige Obasa, matakin ya nuna asalin rikicin da ya barke a majalisar ta 10 a jihar.
‘Yan majalisar dai sun tsige Obasa ne a lokacin da yake kasar Amurka.
Bayan dawowarsa Legas a ranar 25 ga Janairu, 2025, ya kalubalanci cire shi.
Duk da tsoma bakin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC, musamman tsofaffin gwamnonin jihohin Osun da Ogun, Cif Bisi Akande da Cif Olusegun Osoba, ba a warware rikicin shugabancin ba.
Ita ma majalisar ba da shawara kan harkokin mulki a jihar ta kasa shawo kan rikicin, inda wasu mambobin ke ganin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ne kadai zai iya shiga tsakani yadda ya kamata.
Sai dai duk da shiga tsakani da kwamitin sasantawa da Akande ya jagoranta da Tinubu ya shirya domin warware matsalar, da alama rikicin ya kara kamari. Kwamitin dai ya gana da ‘yan kungiyar GAC da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar da kuma ‘yan majalisar, duk da haka bai hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
A ranar Alhamis da ta gabata ne Obasa, wanda bai halarci majalisar ba tun bayan tsige shi, ya koma harabar majalisar a wani mataki na ban mamaki.
Matakin dai ya sanya masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa da sauran al’umma cikin kaduwa, yayin da sabon al’amarin ya kara jefa majalisar cikin rudani.
Duk da shigarsa ofishin, ‘yan majalisa 35 ne suka ki amincewa da Obasa, yayin da ‘yan majalisa hudu suka yi zaman da shi a wannan rana.
A zama na karshe da Meranda ta yi a matsayin shugaban, ta dage zaman majalisar tare da da’awar cewa ta zama shugaban majalisar dokokin Jihar Legas.
Yayin da take bayyana matakinta na yin murabus, Meranda ta ce ta yi hakan ne domin ceto majalisar daga rigingimu da abin kunya da bai kamata ba, tana mai jaddada cewa ta dauki matakin ne don karrama manyan shugabannin siyasa.
Ta yi alkawarin ba za ta rabu da tafarkin mutunci, adalci, rikon amana da hidimar mahaifinta Marigayi Cif Akanni Lawal Taoreed ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp