Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta ayyana Jihar Kebbi a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha aiki cikin tsari da nasara a cikin hukumomkin Alhazai na Nijeriya, Shugaban hukumar, Malam Jalal Ahmed Arabi ne ya bayyana haka a tattaunawsarsa da manema labarai a Jidda ta kasar Saudiya.
Ya ce, Jihar Kebbi ta yi zarra ne a dukkan bangarorin gudanar da aikin Hajji, tun daga jin dadin alhazai daga gida Nijeriya zuwa kasa mai tsarki da samar da ingantaccen masaukai da kuma kula da lafiyar Alhazai.
- Kawar da Shaye-Shayen Tamkar Kawar da Miyagun Laifuka Ne – Kwamandan NDLEA Na Kebbi
- Kotu Ta Dage Shari’ar Matashin Da Ya Kone Masallata A Kano
Sanarwar haka ta fito ne takardar sanarwar da sakataren yada labarai na gwamnan, Alhaji Ahmed Idris ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a Makkah. “Haka ake fatan ganin dukkan jihohi su kasance, muna fatan sauran jihohi za su yi koyi da Jihar Kebbi don samar wa Alhazai jin dadi a yayin gudanar da aikin Hajji a shekaru mai zuwa. Ina mai amfani da wannan damar don jinjina ga Gwamnan Jihar, Dakta Nasir Idris a kan irin goyon bayan da yake ba Hukumar Alhazai ta jihar a karkashin shugabancin Alhaji Faruku Aliyu-Enabo.
“Ina mai buga kirjin cewa, babu wata jiha da ta kyautata harkokin jin dadin Alhazai kamar Jihar Kebbi,” in ji shi.