Babban Ofishin Hukumar Tsaron Al’umma ta Saudi Arabiya ya tabbatar da hana amfani da kowane nau’i tunkuyar gas din girki a sansanin mahajjata da kuma ofisoshin hukumomin gwamnati da ke cikin wurare masu tsarki.
Hukumar tsaron ta bayyana cewa haramcin zai fara aiki ne daga safiyar ranar daya ga watan Zul-Hijjah.
Matakin na hana shiga da kuma amfani da gas din girki a wurare masu tsarki a lokacin aikin Hajji zai kasance tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
Hukumar ta yi gargadin cewa za a kwace duk wasu abubuwan da aka haramta, wadanda suka hada da murhu da tukunyar gas da za a iya amfani da su wajen dafa abinci, tare da jaddada cewa za a yi amfani da hanyoyin da doka ta tanada kan duk wanda aka samu ya saba dokokin.
Tawagar da ke sa ido kan kashe gobara ta hukumar za ta gudanar da rangadi na musamman a dukkan ofisoshin hukumomin gwamnati da cibiyoyin kasuwanci a wurare masu tsarki don tabbatar da cewa ba a yi amfani da gas a harabar Mina, Muzdalifah da Arafat a lokacin aikin Hajji don tabbatar da lafiya da amincin mahajjata.
Matakin hana amfani da gas din girki daga wurare masu tsarki na zuwa ne bisa tsarin kariya da hukumar ta sanya na rage afkuwar gobara a sansanin mahajjata.