Yau Litinin 10, ga Yunin 2024 ita ce rana ta karshe da hukumomin ƙasar Saudiyya suka sanya a mastayin ranar kammala jigilar maniyyata aikin Hajjin bana daga kowace kasa a fadin duniya.
Ana kuma sa ran yau Litinin din da misalin karfe 12 na daren a agogon Saudiyya za a rufe filayen jiragen saman ƙasar 6 daga saukar duk wani jirgin da ya dauko maniyyata daga kowace kasa don zuwa sauke farali a bana.
- Yajin Aiki: NAHCON Ta Gargadi NLC Kan Janyo Cikas Ga Jigilar Maniyyata
- Hajj 2024: Jihar Kaduna Ta Kammala Jigilar Maniyyata Fiye Da 4,000 Zuwa Saudiyya
Ƙasashe da dama waɗan da ba su gama jigilar maniyyatan su ba na ta kokarin ganin sun kammala jigilar alhazan su kafin cikar lokacin da hukumomin kasar Saudiyya suka iyakance.
Filayen jiragen da abun ya shafa sun shafi iya wadanda aka ware don jigilar maniyyatan na bana da suka hada da Riyadh, da Jiddah, da Madina, da Dammam, da Taif, da kuma Yanbu’u.
Hukumomin na kasar Saudiyya sun ce rufewar ba za ta shafi jiragen da suka ɗauko fasinjojin da za su shiga ƙasar domin kasuwanci, da yawon bude ido, da ziyaratar ƴan uwa da dukkan wata lalura da ba ta shafi aikin Hajji ba kamar yadda suka bayyana.