Victor Osimhen na Nijeriya, da Achraf Hakimi na Morocco, da Mohamed Salah na Masar sun shiga jerin ’yan wasan da suka kai matakin ƙarshe na neman kyautar gwarzon dan wasan Afrika ta bana, kamar yadda Hukumar CAF ta tabbatar. Wannan ya dawo da rikici a tsakanin manyan taurarin nahiyar da suka yi fice a kulob da ƙasashensu a kakar da ta wuce.
A bangaren mata kuwa, ’yan wasan Morocco Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, tare da kyaftin din Super Falcons, Rasheedat Ajibade, su ne uku na ƙarshe da ke neman wannan lambar yabo. Hakimi, wanda ke jinya a yanzu, ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa PSG lashe gasar zakarun Turai da kuma kaiwa wasan ƙarshe na Club World Cup, abin da ya ƙara ƙarfafa matsayinsa a jerin ’yan wasan da suka fi fice.
- Hakimin Da Aka Sace A Jihar Kogi Ya Shaki Iskar ‘Yanci
- Osimhen Ya Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai Bayan Zura Ƙwallo 3 A Ragar Ajax
Salah, wanda ya taɓa lashe kyautar sau biyu, ya jagoranci Liverpool wajen lashe Firimiya karo na 20 a bara. Ya kuma ci gaba da nuna gagarumar bajinta bayan samun Golden Boot a kakar 2024–25 da kwallaye 29, abin da ya wuce Alexander Isak na Newcastle, wanda ya tsaya a matsayi na biyu.
Osimhen, wanda yanzu ke Galatasaray, ya kasance cikin shahararrun ’yan wasan Afrika a wasannin gida da na kasa da kasa. Sai dai wasu daga cikin manyan nasarorinsa ba za su shiga lissafi ba saboda ranar da CAF ta sa ta kammala tantance cancanta, wato 15 ga Oktoba. Wannan ya sa hat-trick dinsa a Champions League da Ajax da kuma kwallaye biyu da ya zura wa Gabon a wasan neman gurbin 2026 World Cup ba su shiga cikin ƙididigar bana ba. Duk da haka, yana nan cikin manyan ’yan wasan da suka nuna gagarumar rawar gani a wannan kakar.














