A ranar 26 ga watan Yulin shekara ta 2023, sojoji daga masu gadin fadar shugaban kasar, Nijar suka tsare shugaba Mohamed Bazoum, yayin da wasu gungun sojoji suka sanar da hambarar da shi, suka kuma rufe iyakokin kasar tare da ayyana dokar ta-baci yayin da suka sanar da kafa gwamnatin mulkin soja.
Wannan dai shi ne karo na biyar da sojoji suka yi juyin mulki tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1960.
Kafin juyin mulkin, a baya kasar Nijar ta sha juyin mulkin soji har sau hudu tun bayan samun ‘yancin kai daga Faransa a 1960, inda na karshe ya kasance a shekarar 2010. A tsakanin, an kuma yi yunkurin juyin mulki da dama, wanda na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2021, lokacin da ‘yan adawar soji suka yi yunkurin kwace fadar shugaban kasar kwanaki biyu gabanin rantsar da zababben shugaban kasa Bazoum, wanda shi ne shugaban kasar na farko da ya karbi mulki daga hannun zababben shugaban kasa ta hanyar dimokuradiyya.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karbi ‘Yan Nijeriya 108 Da Suka Makale A Nijar
- Sin Na Adawa Da Kutse Ta Intanet
Bayan juyin mulkin, Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) karkashin shugabancin shugaban kasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ta kakaba wa kasar takunkumin karya tattalin arzki inda aka umarci janye harkokin kasuwanci da tallafi ga kasar.
Tuni Nijeriya ta katse wutar lantarki da take ba Nijar, haka kuma an rufe iyakokin kasar ta yadda kayan abinci da na rayuwar yau da kullum suka daina zirga-zirga.
Wannan ya jefa rayuwar al’ummar kasar cikin matsanancin wahala musamman ganin kasar ta dogara ne a bangarori da dama da abububwa da ake shigowa da su daga kasashen duniya.
LEADERSHIP Hausa, ta tattauna da wani dan asalin kasar da ke Lele Birnin Ader a Jihar Tawa, Malam Yusuf Buzu, inda ya yi bayanin cewa abubuwa sun tabarbare ba kamar yadda gwamnatin sojan ke kokarin nuna wa duniya ba, karfin hali ne kawai suke yi amma al’umma na cikin tasku.
“Muna nan, sai addu’a, rayuwa sai hamdala, gaskiya akwai damuwa sosai game da mulkin sojoji, wallahi mu talakawa muna cikin kuncin rayuwa, da wanda ya yi murnar juyin mulkin da wanda bai yi ba dukkanmu muna cikin wahala, don gaskiya, Shugaban Soji Chani Abdurahaman ba shi da kwarewar tafiyar da kasa.
“A halin yanzu muna fuskantar tsadar abinci ga shi babu kudade a hannun al’umma, an rufe Babban Bankin Kasa, ba abin da ke shigowa Nijar, ga shi kuma masu kudi ba sa jin tsoron Allah, talaka ne kawai yake shan wahala, kuma ‘yan bindiga na cin karensu babu babbaka a kauyuka suna kashe na kashewa suna kama na kamawa, sai wanda Allah ya kare.”
Malam Yusuf Buzu ya ci gaba da cewa, “Nijar na hali mara dadi, abinci ya yi wuya, ka samu kudi amma ba su da darajar da za ka yi wani abu da su. Ana sayar da Shinkafa a kan jika goma shadaya zuwa da rabi kafin juyin mulkin amma a halin yanzu farashin ya kai jikka goma sha bakwai cikin birnin Tawa, a kauye kuma ya kai jikka goma sha tara a wasu kauyukan ma har jikka ashirin yake saboda tsadar kudin mota da ake zirga-zirgar safarar shinkafar.”
Ya kuma ce, wasu ‘yan kasuwar kasar ba su jin tsoron Allah, “duk da cewa, abubuwa da ake ci zuwa yanzu nasu ne wadanda suka ajiye, don yau (ranar Laraba) kusan kwanaki fiye da dari da ashirin ke nan babu kayan da ake shigo da shi cikin kasa saboda rufe iyakoki sakamakon juyin mulki, amma kuma sun tsauwala farashi.”
Sai dai kuma, ya yaba wa wasu daga cikin ‘yan kasuwa da masu kudi wadanda suke tausaya wa al’umma, yana mai cewa, “kai! duniya ta zo karshe, kowa kansa ya sani, mutane daga kansu yaransu, matansu sai daidaiku, kasan ba a yi wa al’umma jam’i, har gobe akwai mutanen kirki, ni kaina nakan wuni ban ci abinci ba a farkon mulkin sojan nan, amma kuma na samu taimako daga mutanen kirki.”
A halin yanzu dai, in ji Malam Yusuf, duk wani dan Nijar abin da ke gabansa shi ne neman samun saukin rayuwa, “a samu samu abinci a cikin sauki a kuma samu zaman lafiya har da ma dukkan ‘yan jam’iyyar PNDS Tarayya wanda juyin mulkin bai yi musu dadi ba, da farko talakawa sun nuna jin dadi amma yanzu murna ta koma ciki.
“Wannan halin da aka shiga ya sanya wasu ke tunani ko Bazoum zai dawo kan karagar mulki duk da cewa, dole shugaba ya yi makiya da masoya in yana mulki amma al’umma Nijjar sun ga ayyukan alhairin da ya yi na tsawon shekara biyu da wata 6”, in ji shi.
Ya kuma ce, babban abin da talaka ke nema daga dukkan masu mulki shi ne zaman lafiya walwala da abin da za a ci cikin adalci.