• English
  • Business News
Friday, May 16, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki

by Maryam Bello
2 years ago
in Sana'a Sa'a
0
Ya Kimar Mace Mara Sana’a Take A Wurin Mijinta?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Jama’a da ke biye da mu a wannan shafi na Sana’a Sa’a barkan mu da warhaka, da fatan za a ci gaba da kasancewa tare da mu a kowane mako.

A yau za mu fara jin ra’ayoyin masu sana’o’i a kan yadda cire tallafin man fetur ke shafar sana’arsu a halin yanzu.

  • Badakala A Kano: An Gano Biliyan 4 Da Ta Yi Batan-Dabo A KASCO
  • ’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban JIBWIS, Sun Sace Mutane 50 A Kaduna

Kamar yadda aka sani dai kusan duk wani abu mai alaka da fetur ya yi tashin gwauron zabi.

Amma da yake an ce waka a bakin mai ita ta fi dadi, bari mu fara da jin ta bakin Shemau Suleiman, da ke sana’ar sayar da Yoghurt a Kaduna Road da ke yankin Suleja a Jihar Nej.

Assalamu Alaikum Warahmatullahi wa barakatuh
Wa alaikumus salam

Labarai Masu Nasaba

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

Yaya Sunan Malamar da kuma wace Sana’a kike yi
Sunana Hajiya Shemau Suleiman. Ina sayar da yoghurt.

Ke ki ke bugawa ko saya kike yi?
Siyan yoghurt din na ke yi Wanda ake bugawa kananu kaman na naira 8 da kuma 43 da kuma naira 18 kuma na ke kankararwa in siyarwa masu sari su Siya sai su siyar daddaya.

Ya yanayin sana’ar ki take yanzu sakamakon cire tallafin Fetur da Gwamnati ta yi:
Gaskiya ba karamin takura muke ciki ba yanzu saboda cire tallafin nan da aka yi ba saboda komai ya haura Yadda ba a tsammani da gaba daya na yoghurt ana siyar mana daga kamfani 950 wani kamfanin 1000 yanzu ya dawo na naira 8 ya dawo 1400,2000 na 43.

Ya yanayin ciniki kuma yake:
Gaskiya sai dai dua’i da kuma godiyan Allah.kin GA sai an je kamfani an siyo GA kara farashin da su kayi saboda tashin Kaya a kasuwa Ka biya Mai Baro ya kwaso ya kawo maka gida,Ka saka cikin freezer ya kankare Ka bayar wa masu sari su kuma suna fadar kudin mota ya Karu Inda suke kaiwa su siyar na da nisa ga kudin mota ya yi tsada ba su samun riba kamar yadda suke samu da.wani Lokacin ma har fadawa su ke yi a ciki sakamakon sun siyar da Kaya sun ci abinci GA kudin mota da ya Karu sai ki ga BA su rage da KO sisi BA.

Ya bambancin cinikin da kike samu ada da yanzu:
Gaskiya sana’a ce da ake samu sosai musamman idan Ka na da kayan aiki wato freezai KO kuma cold room za Ka samu sosai saboda na Gina gidaje da sana’ar nan kuma hatta cold room din da na Fara da guda biyu ne Amma yanzu da taimako Allah Ina da cold room 3 a gida kuma Ina da shago ma na dauki masu tayani siyar da kaya

Ya ya kuke fama da wutar lantarki?
Alhamdulillah muna samun wuta sosai sai dai matsalar su ma NEPA kudin wutan da suke kawo mana yayi yawa sosai don bill wani Lokacin Har 100000 su ke kawowa kin GA shima Yana Kara ja da sana’ar Baya.

Wane kira za ki yi ga mata masu zaman jiran sai an kawo an ba su?
Mata Lokaci ya yi da ya kamata mu tashi mu nemi Abin yi saboda ya na kara wa mace daraja a gun mijin ta tunda ba sai kin jira ba kuma kina taimako shi ne tunda in kin yi abu a gida AI kin toshe baban abu ne tunda ko riga mai kyau aka gan ki da shi za a ce shi ya saya miki.

Wane kira za ki yi wa gwamnati
Ni dai roko na Allah ya kawo mana karshen wannan matsalar kuma su taimaka don rage kudin Fetur jama’a na wahala.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: HaliKasuwanciSana'o'iYanayi
ShareTweetSendShare
Previous Post

Wakilin Sin A MDD Ya Yi Kira Da A Dagewa Wasu Kasashen Afirka Takunkumai

Next Post

Tabbas Mun Samu Tangarda Wurin Shigar Da Sakamakon Zaben 2023 –INEC

Related

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

3 months ago
Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Labarai

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

6 months ago
Akwai Dimbin Alhairi A Harkar Kasuwanci Na Kirifto – Khadija Ahmad
Labarai

Akwai Dimbin Alhairi A Harkar Kasuwanci Na Kirifto – Khadija Ahmad

9 months ago
Dangote Ya Soki Sabon Tsarin Gwamnatin Tinubu
Manyan Labarai

Dangote Ya Soki Sabon Tsarin Gwamnatin Tinubu

11 months ago
Shara
Sana'a Sa'a

Sarrafa Daskararriyar Shara

2 years ago
Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki (3)
Sana'a Sa'a

Halin Da Masu Kananan Sana’o’i Ke Ciki (3)

2 years ago
Next Post
Zaben Gwamnoni: INEC Ta Gargadi Jam’iyyun Siyasa Kan Tada Tarzoma

Tabbas Mun Samu Tangarda Wurin Shigar Da Sakamakon Zaben 2023 –INEC

LABARAI MASU NASABA

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

Masu Garkuwa Sun Nemi Miliyan ₦30 Don Sako Shugaban APC A Ondo

May 16, 2025
Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

Dalilin Tsame Daya Cikin Uku Na Ma’aikatan Ƙasar Nan A Tsarin Sauye-sauyen Biyan Haraji – Czar

May 16, 2025
Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mahajjaci

May 16, 2025
Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

Tinubu Ya Kira Taron Manyan Kafafen Yada Labarai Kan Samar Da Wadataccen Abinci

May 16, 2025
Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

Abin  Da Ya Sa Ilimi Yake Da Muhimmanci Ga Rayuwar Al’umma (1)

May 16, 2025
Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

Rashin Tsaro Da Raba Wa Manoma Kayan Aiki Kan Lokaci Na Baraza Ga Wadata Kasa Da Abinci

May 16, 2025
Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

Kasar Sin Ta Yanke Shawarar Hana Taiwan Halartar Babban Taron WHO Na Bana

May 15, 2025
Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

Faɗuwar Farashi: Masu Ɓoye Abinci Don Ya Yi Tsada, Asara Kawai Suke Ƙirgawa , In Ji BUA

May 15, 2025
Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

Sin Ta Bukaci Amurka Ta Dakatar Da Harajin Sashe Na 232

May 15, 2025
Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

Xi Ya Taya Shugaban Togo Murnar Karbar Ragamar Shugabanci

May 15, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.