Mataimakin shugaban kasar Sin, Han Zheng, a cikin jawabinsa a zauren taron MDD a jiya Alhamis, ya yi kira ga kasashen duniya da su tsaya tsayin daka kan ra’ayin bangarori daban-daban, da kyautata tsarin tafiyar da harkokin duniya.
Da yake jawabi a babbar muhawara a gun babban taron MDD karo na 78, Han ya ce kamata ya yi kasashe mambobin MDD su tabbatar da daidaito da adalci, da kiyaye zaman lafiya da tsaro, da tabbatar da moriyar juna, da samar da nasara da ci gaba ga kowa da kowa, da hada kai, da ciyar da wayewar bil Adama gaba, kuma su kasance masu gaskiya ga tsarin hadin gwiwa da inganta tsarin shugabancin duniya.
Da yake karin haske game da batun ci gaba, Han ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yin hadin gwiwa a fannin shirin shawarar ziri daya da hanya daya da kuma ajandar ci gaba mai dorewa ta 2030, inda ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen gina al’ummar duniya baki daya. Ya kamata kasashe da al’ummomi mabambanta su yi rayuwar ci gaba tare ta hanyar mutunta juna, su yi amfani da karfin juna wajen samun ci gaba, da cimma nasara ta hanyar hadin gwiwa.
Dangane da batun kare hakkin bil Adama, mataimakin shugaban kasar ya ce, ya kamata kasashen duniya su ciyar da harkokin kare hakkin bil Adama na kasa da kasa gaba ta hanyar hadin gwiwa, tare da yin adawa da siyasantar da batun hakkin bil Adama.
Han ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne, ya kamata duniya ta tsaya tsayin daka wajen adawa da amfani da hakkin dan Adam da dimokuradiyya a matsayin wani makamin siyasa wajen tsoma baki cikin harkokin wasu kasashe.
Ya kuma bukaci kasashen duniya da su karfafa wakilci da muryar kasashe masu tasowa da tabbatar da gudanar da shugabancin duniya cikin adalci da daidaito. (Yahaya)