Fara harkar kasuwanci nada saukin gaske amma tabbatar da ci gaban kasuwancin ne babbar kalubane a Nijeriya. A yau za mu kawo muku hanyoyin bunkasa kasuwanci a cikin sauki a Nijeriya.
Za kuma mu duba dabarun da mutum ke bukata don bunkasar harkar kasuwancinsa musamman ganin Nijeriya na daya daga cikin wuraren da harkokin kasuwanci ya fi bunkasa kuma yake fuskantar kalubale da dama a duniya.
- Buhari Zai Kaddamar Da Aiki Sannan Ya Gana Da ‘Yan Kasuwar ‘Monday Market’ A Borno
- Bunkasar Da Kawancen Kasuwancin Sin Da Afirka Ke Yi Ta Nuna Gaba Za Ta Fi Kyau
Akwai dalilai da dama da zai karfafa mutum shiga harkar kasuwanci a Nijeriya wadanda suka hada da bukatar samun rufin asiri a wannan lokacin da kowa keji a jikinsa, musamman in kasuwancin ya samu bunkasar da ake bukata, tafi da kasuwanci na bukatar mutum ya tsayu tare da bibiyar yadda wasu bangarori ke tafiyar da nasu kasuwancin, ta haka dan kasuwa zai tafi daidai da yadda ake tafiya. Ya kuma kamata mutum ya samu cikakken tsari na tafiyar da kasuwancinsa.
Tafiyar da kasuwanci na bukatar mutum ya sadaukar da wasu lokutta nasa, dole ya raba lokuttan tsakanin kasuwancin nasa da kuma rayuwarsa. Ka samar da lokaci na iyali da sauran harkokin rayuwar ka. In ka fara tafiyar da harkokin kasuwancin kan kada kan, to ka za ma shugaban kan ka ke nan, babu sauran daukar dokoki ko umarni daga wani, yanzu kai ne shugaban kanka da kan ka.
Yayin da ka hada wadannan matakai wadanda suke zama tamkar ginshiki na tabbatar da harkar tafi da kasuwancin ka a Nijeriya. Kana bukatar sanin wasu matakai da za su taimaka maka wajen samun nasarar tafi da harkokin kasuwancin sun kuma hada da;
1. Ka tabbatar da zabar nagartattun mutanen da za su taimaka maka tafiyar da kasuwancin ka ba tare da nuna bambanci ba, ka kuma rike karfinka na ikon dauka da korar duk wanda ya nemi ya kawo wa kasuwancin cikas ko zagon kasa. Ka nastu sosai wajen daukar ma’aikata domin akwai wadanda za su shigo ne domin su nakasa ka su yi tafiyarsu.
2. Dole ne, in ana son samnun nasara a kasuwanci a Nijeriya mutum ya iya tafiyar da kudaden kasuwancin sa. Ka samu littafi da zaka rika shigar da dukkan bayanan da suka shafi kudaden da ke shigowa da kuma wadanda suke fita, ta haka zaka san ko kana cin riba ne ko kuma akwai matsala. In har ba hakaba, ba zaka san lokacin da zaka shiga cikin ribar ka ba.
3. Ka bude kofofin karbar shawara domin shawara na taimakawa wajen ci gaban kasuwanci, ka karbi shawara daga abokan huldar ka da ma’aikatan ka hakan zai taimaka maka sanin cikakken irin abin da suke so domin ka kara kaimi wajen gamsar da abokan huldar ka
4. Sauran matakai na bunkar kasuwanci a Nijeriya sun hada da, tallata harkokin kasuwancin ka ta kafafen sadarwa na zamani, wannan na da muhimmanci in aka lura a wannan zamanin kusan kowa yana hulda da kafafen sadarwa na zamani, ka nemi kafar da ta dace da irin kasuwancin ka, ka yi amfani da shi wajen sanar da al’umma irin hajar da da ke sayarwa, nan take zaka ga yadda mutane za su rinka tuntubarka domin neman karin bayani.
5. Halartar tarukan kara wa juna sani a kan harkokin kasuwanci yana da matukar muhimmanci. Ka zama mai neman karin ilimi a koda yaushe tare da neman karin yadda zaka bunkasa kasuwancinka.
6. Tattara bayanai game da abokan hudar ka, hakan zai taimaka maka samar da abubuwan da suka yi daidai da bukatunsu. Haka kuma bayanan za su taimaka maka samar da sauye-sauyen da za su kara jawo maka abokan hulda sosai.
7. Sanin salon rike tsofaffin abokan hudarka, kasuwanci ba wai yana habbaka ta hanyar shigowar sabbin abokan hulda ne kawai ba, amma yadda ka rike tsofafin abokan hulda yana da matukar muhimmanci a ci gaban kasuwancin ka. Saboda haka ka samar da hanyoyin rike tsofaffin kwastomomin ka, za su taimaka bunkasar harkar kasuwancin ka.