Gwamnatin tarayya, ta kaddamar da shirye-shirye guda biyar; domin dakile karancin abinci tare da daidaita farashinsa a 2025.
Babban Ministan Aikin Gona da Samar da Wadattacen Abinci Abubakar Kyari ne, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja.
- Faduwar Darajar Naira Ya Haifar Da Raguwar Kayan Da Ake Shigowa Da Su Nijeriya
- Sinawa Kimanin Miliyan 1.85 Za Su Rika Zuwa Yawon Bude Ido a Ketare Kullum Lokacin Hutun Bikin Bazara
Inda ya bayyana cewa, gwamnatin ta mayar da hankali wajen ganin an kara bunkasa noma da kuma magance wa manoman kalubalen da suke fuskanta na gaza noman wadataccen amfanin gona.
Kyari ya yi nuni da cewa, dogaro kadai a kan kasafin kudi, bai zai iya wadatar da wannan fanni na noma ba.
Wadannan shirye-shiye biyar sun hada da:
1- Gabatar Da Noman Alkama A Kakar Damina: Kyari ya ce, bisa kari da ci gaba da ake yi na shirin noman Alkama na rani a wasu jihohin kasar, za kuma a rungumi noman Alkama na damina, musamman a Jihohin Kuros Riba, Filato da Taraba.
“Wannan ne karo na farko da jihohin da ke Kudancin Kasar nan, za su bi sahun jihohi sha biyar da ake noman Alkamar”, in ji Kyari.
Sannan ya sanar da cewa, daukin da gwamnatin tarayya ta samar a shirin noman Alkamar na rani kashi na daya, ya kare a ranar 27 ga watan Disambar 2024.
“A karkashin shirin, mun taimaka da hektar noman Alkama 150,000, wanda hakan ya nuna cewa, manomanta 300,000 ne suka amfana da wannan hekta”, in ji Ministan.
Kyari ya kara da cewa, an kuma sayarwa da manomanta Iri kan farashi mai sauki, wanda aka yi masu ragi daga kashi 25 zuwa kashi 75.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatin ta kuma sayarwa da manoman takin zamani a kan farashi mai sauki, wanda ya kasance a kan kashi 50 cikin 100.
A 2024, Kyari ya bayyana cewa, gwamnatin a karkashin shirin bayar da daukin noma na kasa, wato na tura wa manoma kudi ta hanyar amfani da manhajar zamani (NAGS-AP), manoman rani 400,000 ne gwamnatin ta taimakawa daga 2024 zuwa 2025.
2- Kwangilar Shigo Da Taraktocin Noma 2,000 Daga Kamfanin Belarus:
Kyari ya bayyana cewa, tuni wadannan taraktoci sun fara shigowa cikin wannan kasa, ta hanyar tashar jiragen ruwa da ke Legas, inda ya ce, za a raba wa manoman taraktocin ne da nufin kara bunkasa noman Tumatir a yankunan Kudu Maso Gabas da kuma na Kudu Maso Yamma.
Ya ce, taraktocin, a daya daga cikin yunkurin gwamnatin na karfafa wa manoman yin noman zamani.
3- Gyara Tsarin Bayar Da Kudin Rancen Yin Noma Na Bankin Aikin Noma (BoA):
Kyari ya sanar da shiry-shiyen gyara tsarin bayar da rance kudin yin noma na Bankin Aikin Noma, inda ya ce, Bankin wanda ke da rassa a mazabu 109 na kasar nan, za a saita shi don ya rika bayar da rance ga kanannan manoma.
A cewarsa, jawo abokan hadaka kamar irin su, Gidauniyar Bunkasa Aikin Noma ta Kasa da Kasa (IFAD), hakan zai taimaka wajen samar da damar samun kudade,
4- Kara Inganta Noma Da Kayan Aiki Na Zamani:
Kyari ya bayyana cewa, wannan na daya daga cikin burin Shugaba Tinubu, na samar da taraktocin noma ga manoma.
5- Magance Asarar Da Manoma Ke Yi Bayan Girbe Amfanin Gona:
Kyari ya sanar da cewa, za a samar da shiye-shirye tare da tanadin guraren adana amfanin gona da aka girbe, musammna domin magance asarar da manoman ke yi, da ta kai ta kimanin Naira tiriliyan 3.5, inda ya ce, wannan matakin na daga cikin burin da Tinubu ke son cimma a 2025.