• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Mata Za Su Bi Don Gyara Jikinsu

by Bilkisu Tijjani and Abubakar Sulaiman
12 months ago
Mata

Assalamu alaikum masu karatu, barkanmu da sake haduwa da ku a wannan mako a cikin shirin na mu mai farin jini da albarka na Adon Da Kwalliya.

 

A yau na kawo muku wasu hanyoyi wanda za a bi don gyaran jiki ba tare da an kashe kudi a shagon kayan kwalliya ba. Ya kamata mata su koyi dabaru da dama domin taimaka wa maigida. Idan maigida ya saba ba da kudin sayen kayan kwalliya, ranar da babu kuma sai a hakura a gwada daya daga cikin ababen da muke kawo muku na gyaran jiki.

  •  ‘Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Kulle Matashi A Kejin Kare
  • ‘Mata Network’ Za Su Yi Taron Su Karo Na Shida A Kano

Idan ki tashi gyara gashi za ki iya hada ayaba da kwai sai a kwaba su sosai, sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin, sannan a wanke.

 

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

Domin gyara farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi matukar kyau sosai.

 

Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai santsi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin, sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya ma a sati za a ga canji.

 

Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rika shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka bakin da ya bayyana a wasu gabbai ko sassan fata.

 

Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rika dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.

 

Man kwa-kwa na matukar gyaran zubewar gashin kai, za a iya shafa man kwa-kwa a fatar kai, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.

 

Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.

 

A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai. Sannan a rika shafawa a kan kurajen fuska. Yin hakan na kashe su sosai. Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
IPAC: Tasiri Ko Rashin Tasirinta A Siyasar Nijeriya

IPAC: Tasiri Ko Rashin Tasirinta A Siyasar Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.