• English
  • Business News
Sunday, September 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Za A Taimaka Wa Malamai Inganta Aikinsu (3)

by Idris Aliyu Daudawa
1 year ago
in Ilimi
0
Hanyoyin Da Za A Taimaka Wa Malamai Inganta Aikinsu (3)
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

5. Samar Da Yanayin Da Zai Kara Wa Malamai Kwarin Gwiwa

Wurin da Malaman makaranta suke aiki ya na bada gudunmawa kwarai wajen bunkasa aikinsu, sai dai kuma idan  basu samun lokaci na hutawa  ga kuma gajiya, irin hakan ba zai haifar da da mai ido ba domin ba za su samu kwarin gwiwa ba wajen aikinsu.Idan mutum na neman yadda za  ka taimakawa Malamai  wajen gabatar da aikinsu sai ka fara samar da ko tunanin samar da duk abubuwan da  za su taimaka.

Lura da yadda ake tafiyar da aki a makarantar ka.Ka yi sauye- sauye idan kana ganin Malamanka ayyukan da suke yi sun yi masu yawa.Malaman suna kara samun kwarin gwiwa ne idan yadda suke gudanar da ayyukansu ana taimaka masu da abubuwan da za su ja hankalinsu su kara zage – damtse ga aikinsu.Makarantu ko kwaleji sau da yawa Malaman makaranta

6.Ka Tabbata Malaman Da Ke Aiki Karkashinka Ba Su Fuskanatar Matsala Wajen Gudanar Da Aikinsu

Bayan sun yi aiki a makaranta ko kwaleji Malaman makaranta sau da yawa suna korafin cewar basu samun lokacin da za su kasance da ‘ya’yansu da sauran Iyalai, rashin tsara yadda za ayi aiki kan iya sa Malamai su gaji da rashin sha’awar yin aikin kamar yadda ya dace.

Labarai Masu Nasaba

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

Ka lura sosai da irin wannan al’amarin wajen taimaka wa Malaman makarantar ka yadda za su tafiyar da aikinsu da abubuwan da suka shafe su ba tare da daya ya cutar da daya ba.

Ka yi bincike domin ka gano wadannan abubuwan

Wadanne abubuwa ne Malaman makaranta suke fuskanta a wurin aiki?

Wadanne taimako suke bukata domi samun maslahar matsalar?

Shawarwarin da suka bada na iya taimakawa wajen gano bakin zaren.

Da Zarar ka gane yadda matsalolin suke sai ka samar da wasu hanyoyin da kake ganin  za su ko na iya taimakawa wajen maganin matsalolin da suke fuskanta.Idan yadda Malaman makaranta ke gudanar da ayyukansu babu wata matsala da kuma samun isasshen lokacin da za su kasance da iyalansu,hakan zai sa su kara maida hankalinsu wajen gudanar da aikinsu cikin farinciki.

Abu daya misalin da zai bada sha’awa shine Duolingo, ita ce hedikwatar a Pittsburgh,Pennsylbania,ba kawai su  samu nasara wajen fafutukarta ta bunkasa koyon harshe ta kafofin koyo na zamani.Amma an bada  fifiko ko muhimmanci wajen samar da abubuwan da za su jawo hankalin ma’aikata maida hankalinsu wajen gudanar da aiki yadda ya dace.Kamfanin ya lura da amincewa da muhimmancin samar da duk abubuwan da suka dace tsakanin ayyukansu da suka koya  a makaranta da lura da iyalansu.

Mai da hankali ko sa ido na yadda za a dudanar da ayyuka kamar dai irin salon Duolingo da suka hada da yadda abubuwan suke a tsarin yadda ake tafiyar da ayyuka da kuma tsare- tsare na Kamfani.Wadannan sun hada da tsare- tsare da za su taimaka wajen samar da awowin yin aiki, ba ma’aikata amfani da tsarin aikin da zai taimaka wajen cimma burinsu ko bukatunsu.

Da ya ke ya gano duk abubuwan da za su  yi maganin matsalolin da ma’aikata suke fuskanta da suka hada da abubuwan da ake sa ran ma’aikata za su yi ko ya kamata su yi sai Duolingo shi ma ya bada ta shi gudunmawar yadda kowa zi kasance ya amince da kuma jin dadin shi al’amarin gaba daya.

Bugu da kari kamfanin ya maida hankali kan yadda al’amuran suke kai har ma abin ya zarce yadda ake bukata na nau’oin ayyuka.Duolingo  ya maida hanakali yadda ya dace ayi saboda kuwa ya lura da cewar duk wurin aikin da aka samar da abubuwan da za su taimakawa masu gudanar da aikin wajen maida hankalinsu ga yin aikin kamar yadda ya dace, ko shakka babu za  a samu cimma buri ta kowane bangare.

7.A Rika Bikin Ranar Haihuwa Da Shekarun Da Aka Yi Aiki

Yin biki na muhimman ranaku na Malamanku hakan zai dauki lokaci mai tsawo wajen bunkasawa Malamai ko kara masu kwarin gwiwa.

Ana iya biki ranar haihuwa, shekarun aiki da duk wani ci gaban da aka samu, kamar aure, ranar Malamai ta duniya da sauransu saboda yin hakan zai sa suma su san an dauke su da muhimmanci.

Bikin wani ci gaba ko wani abu na ma’aikatanka zai sa su gane cewa an dauke su da muhimmanci, hakan zai rika sa su gane cewa suma naka ne.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kalubalen Da Manyan Kafafen Labarai Ke Fuskanta A Yanzu – Shugaban MacArthur

Next Post

Hada Layuka Da NIN: MTN Ta Kulle Layuka Miliyan 4.2 A Nijeriya

Related

ASUU
Ilimi

Malaman Jami’o’i Sun Zama Abin Tausayi —Kungiyar ASUU

13 hours ago
Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai
Da ɗumi-ɗuminsa

Jami’ar Bayero Ta Yi Rashin Fitaccen Masanin Ilimin Harshe, Farfesa Hafizu Miko Yakasai

3 days ago
Lambar Yabo Ta CON: Buni Ya Zama Zinare Bashi Da Maboya
Ilimi

NTIC Ta Jinjina Wa Gwamna Buni Kan Taimako A Bangaren Ilimi

1 week ago
Hukumar SUBEB Ta Yi Kira Ga Al’umma Da Su Sa ‘Ya’yansu Makaranta
Ilimi

Hukumar SUBEB Ta Yi Kira Ga Al’umma Da Su Sa ‘Ya’yansu Makaranta

1 week ago
Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu
Ilimi

Yajin Aiki: Kungiyar ASUP Ta Ba Gwamntin Tarayya Wa’adin Kwana 21 Ta Biya Masu Bukatu

2 weeks ago
Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima
Ilimi

Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

3 weeks ago
Next Post
Hada Layuka Da NIN: MTN Ta Kulle Layuka Miliyan 4.2 A Nijeriya

Hada Layuka Da NIN: MTN Ta Kulle Layuka Miliyan 4.2 A Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

Makaman Rasha Masu Gudun Walkiya Da Ke Yi Wa Ƙasashen Turai Barazana

September 7, 2025
Kudin Ajiya Na Sin A Ketare Ya Karu A Watan Agusta

Kudin Ajiya Na Sin A Ketare Ya Karu A Watan Agusta

September 7, 2025
El-Rufai Ba Mai Gidana Ba Ne – In Ji Gwamna Uba Sani⁩

El-Rufai Ba Mai Gidana Ba Ne – In Ji Gwamna Uba Sani⁩

September 7, 2025
Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga Kachalla Balla Da Wasu Biyar A Kogi

Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga Kachalla Balla Da Wasu Biyar A Kogi

September 7, 2025
An Fara Jigila Kai Tsaye Daga Lardin Zhejiang Na Sin Zuwa Nahiyar Afrika

An Fara Jigila Kai Tsaye Daga Lardin Zhejiang Na Sin Zuwa Nahiyar Afrika

September 7, 2025
Kungiyoyin Gasar Firimiya Sun Kashe Dala Biliyan 4 A Kasuwar Saye Da Sayar Da ‘Yan Kwallo Ta Bana

Kungiyoyin Gasar Firimiya Sun Kashe Dala Biliyan 4 A Kasuwar Saye Da Sayar Da ‘Yan Kwallo Ta Bana

September 7, 2025
Ƴan Ta’adda Sun Kai Hari Kachia, Sun Kashe Mutum 8, Sun Sace Wasu Da Dama

Ƴan Ta’adda Sun Kai Hari Kachia, Sun Kashe Mutum 8, Sun Sace Wasu Da Dama

September 7, 2025
NWDC Za Ta Sanya Hannu Kan MoU Na Dala Miliyan 200 Don Inganta Noma

NWDC Za Ta Sanya Hannu Kan MoU Na Dala Miliyan 200 Don Inganta Noma

September 7, 2025
Sin Da AU Sun Yi Alkawarin Daukaka Tsaro Da Adalci A Duniya

Sin Da AU Sun Yi Alkawarin Daukaka Tsaro Da Adalci A Duniya

September 7, 2025
Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

Duk Wanda Ya Girme Ni Ubangidana Ne A Harkar Fim – Hauwa Garba (2)

September 7, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.