8.Taimaka Musu Da Abubuwan Da Za Su Inganta Aikinsu
Malamai suna bukatar abubuwan da za su taimaka masu wajen taimakn dalibai domin su maida hankali kan abin da ake koya masu.Malamai suna samun kwanciyar hankali da sanin kosu su wanene idan suna koyarwa a kananan azuzuwa ko babbar Makarantar Sakandare musamman ma idan aka samar masu abubuwan da suka dace na aikinsu.
Samarwa Malamai kayan da suka dace kamar na taimakawa aiwatar aikinsu fasaha da dai sauransu domin koyawa dalibai kamar yadda ya dace, hakan yana taimakawa wajen bunkasa ilmi mai inganci.
Idan aka samar da hanya wadda za ta sa Malaman makaranta gudanar da aikinsu ba tare da matsala ba, wannan zai kara masu kwarin gwiwa.
Alal misali al’amarin koyarwa ko Malanta a Amurka ana taimakawa masu yiwa kasa hidima, domin su samu nasara a azuzuwa ta hanyar tsare- tsaren ci gaba.Irin cikakken tsarin taimako ya kunshi horarwa ta lokacin bazara, wadda horarwa ce da ake yi ma wadanda suke yin aikin koyarwa.
Horarwar da ake yi za ta tabbatar akwai tsari na maganin bukatu da matsaloli.Akwai taon karawa juna ilimi da sauran wasu hanyoyi domin ci gaba da horarwa domin tabbatar da ci gaba da samun horo wanda zai taimaka ta hanyar kara ilimin su masu koyarwar wato Malaman makaranta ke nan.Duk wata hanya ta samar da karuwar ilimin da aka karanta na bada dama ta yadda su Malaman za su kara koyon sabbin dabaru wadanda suka kamata ayi amfani da su domin cimma buri.
Shi tsarin TFA ya bada dama masu su al’ummar garin su bada tasu gudunmawar da za ta taimaka ta yadda su kwararru ta bangaren da ya sha ilimin koyarwa za su yi musayar ra’ayi da neman shawara idan bukatar haka ta taso. Irin wannan matakin na TFA wajen jajircewa ta bunkasar ilimi ta yadda ake taimakawa Malaman makaranta da dabarun koyarwa da za su taimake su, su ma idan sun zo koyar da dalibansu abin zai zo masu da sauki, irin hakan kuma ba yadda za a hada shi da irin koyarwa da babu dabarun da za su taimaka wajen fahimtar abin da ake koyo.
Ta hanyar ko tsarin a koyar a Amurka TFA (Teach Fo America)tsarin ba kawai ya tsaya ne kan nunawa su Malamai yadda za su shirya kadai bane domin koyarwa domin samar da ilimi, da akwai ma tsari na shirin bautawa al’umma domin samun sauyin da zai kawo ci gabansu.
- A Rika amincewa da shawarwarin da suka ba da na yadda aikin nasu zai ba da abin da ake bukata
Malamai suna mu’amala ta kut da kut a kowace rana don haka sun san hanyoyin koyarwa da tsare- tsare wadanda za su taimaka masu, bugu da kari kuma za su iya sanin kwazo ko ragwancin kowane dalibi.
Don haka mutanen da suka fi kamata su bada shawarwarin koyarwa sune Malaman makaranta idan kuma su ka bada shawara kada ayi watsi da shawarwarin nasu na nuna yin na’am da su.
Idan Malamai ba su son bada shawarwari sai a gaiyace su wajen taron samo mafitar da tafi dacewa,a kuma ce su bada shawarwarinsu da suke ganin in an yi amfani da su za a cimma manufa.
Lokacin da suka gane an san muhimmancinsu wajen samar karuwar ci gaba wajen koyar da dalibai hakan zai kara masu kwarin gwiwa, su tabbatar da daga krshe za’a samu nasara. Daya daga misalin shine EdTech giant is Amplify.
Amplify shi ba kawi ya tsaya a kan al’amarin samar da ilimi ba wata kafa ce da ta lura da muhimmancin kwarewar Malamai,wajen yadda suka gane gudunmawar da suke badawa tana da wani muhimmin al’amari na koyarwa ta hanyar da aka koya masu.Amplify bada wasa take ba wajen karba da hannu biyu shawarwarin da Malamai suka bada musamman ma wadanda za su taimaka wajen bunkasar ilimi.