Ci gaba da makon jiya…
12.Taimakawa Malamai Domin yadda za su ci gaba wajen aikinsu na Koyarwa
Taimaka wa Malamai wajen ci gabansu na daya daga cikin matakan da suka fi dacewa ayi amfani dasu domin suna daga cikin hanyoyin da za su jawo hankali su yi aiki tukuru.
Kamar sauran ma’aikata Malamai suma suna da bukatar ci gaba cikin aikin da suke yi na koyarwa,suma za su so yin wani babban kwas domin bunkasa a sana’arsu ta koyarwa.Sai dai kuma yawancinsu aiki yai masu yawa basu da lokaci ko abin da za su yi mafani da shi wajen taimakawa kansu.
Ana iya taimaka masu ta wadannan hanyoyin:
Basu taimako na kudi domin su bunkasa iliminsu.
Samar ta wata hanya mafi dacewa ta za su taimakawa kansu wajen halartar tarurruka da sauran abubuwan da za ayi a aji wadanda za a iya amfani da su domin kara masu girma ko mukami
Idan ana taimakawa Malamai wajen bunkasa iliminsu na koyarwa za su kasance ko wane lokaci hankalinsu kan yadda makarantarka za ta ci gaba da bunkasa koda wane lokaci.
Alal misali Coursera tana samar da hanya ta bunkasar ma’aikatanta wadanda yawancinsu sun maida hnkalinsu ne kan bunkasar da cimma muradan ma’aikata da ma’aikata.Sa ido kan yadda za ayi maganin matsalolin da maa’ikata ke fuskanta darektan koyo da ci gaba na Coursera Ian Stuart,ya yi amanna ne da muhimmanci abu da ya hada horarwa da da manyan muradan kamfani.Alal misali bullo da sabuwar manufar kamfani daga Shugabannin Coursera suma samar da masana kan wata karuwar da aka samu sanadiyar tarurrukan karawa juna ilimi, abin da za a hada shi da kafa ta koyo akan akidar kamfanin take wajen kulawa da ma’aikatanta.
Kamfanin ya amince da wani tsari na Shugbanci musamman ma, a tsakanin ma’aikata da suke matasa da suka kasance aikinsu ke nan na farko bayan sun kammala Kwaleji.Stuart ta san amfanin koyawa ma’aikata su yi amfani da sababbin tsare-tsare domin cimma biyan muradi da maganin matsaloli ba tare da neman taimako ba.Courser bata wasa da al’amarin Shugabanci ta kowane mataki inda take kalubalantar ma’aikata su kasance kamar Shugabanni ba tare da yin la’akari da kowane irin mataki su ke na tsarin ma’aikatan kamfanin ba.
Coursera ko shakka babu bata yin wasa da duk wata damar data samu dangane da shirin ta na fuskantar duk wani abin da ka iya tasowa ta hanyar tsarinta na koyo da ake kira da sunan Coursera saboda kasuwanci for Business.
13. Samar da kafa ta yadda Malamai za su san ko ana fahimtar darussan da suke koyawa.
Samar da kafa ta samun bayani kan lamarin da ake ciki a wurin aiki na da muhimmanci domin yana ba Malamana makaranta kwarin gwiwa su kasance suna farin ciki a wurin da sue aiki.
Wannan lamarin ya dace ya zama biyu ba kuma wata kunbiya- kunbiya,manufar shi tsarin ya kunshi girma da ci gaba , ba wai a domin a samu wurin da Malamai basu kyauta ba ko a ga laifinsu.
Abin ba tsaya bane kan samun bayan ikan halin da ake ciki ba akwai bukatar taimakawa domin su Malamai su samu kwarin gwiwa ko su kara hazaka kan abubuwan da suke koyawa dalibai ko’yanmakaranta,yana iya kasancewa haorar da su,ko kudade da sauran abubu saboda koyarwa.
Bugu da kari ana iya sa su samar da kawo hanyar da za a taimaka kamar yadda za su bada shawarwari.
14.A Rika lura da yadda Malamai suke gudanar da ayyukansu lokaci zuwa lokaci
Lura da yadda Malamai suke gudanar da aikinsu wannan ma wata hanya ce za a rika lura da irin kokarin da Malamin makaranta yake yi wajen kare ‘yancin dalibansa.Idan ba irin hakan kake yi a makarantarka ba lamarin ba zai baka dama ta sanin halin da ake ciki ba.
Idan kana bibiyar ayyukan Malamanka wata hanya ce da za sa kowane lokaci su kasance a cikin shirin yin aki yadda ya dace tun daga zuciyarsu,sai da kuma in har baka yin wannan tunanin duk wata niyyar da kake da ita ta sa ko yaushe su kasance cikn karin gwiwa ba za ka samu nasarar hakan ba.
Kasance kana da tsari mafi dacewa da za ka rika auna kwazon kowane Malami da yadda hakan za ta yiyu,su Malaman ya zama sun san yadda za ka gane kwazon yadda suke gudanar da aikinsu.