Shugaban Kwamitin Bincike a cibiyar binciken aikin noma IAR na, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, Farfesa Rabiu Adamu, ya ce hanyoyin noma na gargajiya ba za su iya samar da biyan bukatar abinci a Nijeriya ba, don haka ba mai dorewa ba ne, musamman saboda yawaitar jama’a da raguwar filayen noma.
Ya ce Nijeriya, wadda ita ce kasa mafi yawan jama’a a Afirka, tana samar da tan miliyan 12.4 na masara, alhali bukatar kasa ita ce tan miliyan 18.
- Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
- Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari
Domin magance gibin, farfesan ya ce gwamnati ta amince a kawo sabon iri na masara mai yawan amfanarwa, mai jure fari da kwari.
Ya ce, “Nijeriya har yanzu na bukatar ta inganta yawan amfanin gona a kowane fadin fili. A halin yanzu, a kan hekta daya, ana samun kasa da tan 3, don haka akwai bukatar a inganta wannan, domin kaucewa gurbacewar kasa ta hanyar fadada birane, gina hanyoyi da sauran abubuwa kamar hamada sun rika raguwa da filayen noma.
Don kara yawan amfanin gona, ana bukatar irin shuka mai yawan amfanarwa, wacce ba ta bukatar magungunan kashe ciyawa ko kwari, ko ma takin zamani,” in ji Adamu.
Dangane da fargaba game da karancin abinci na amfanin gona da aka canza jinsinsu (GMOs), farfesan ya ce domin tabbatar da lafiyar abinci da kare lafiyar jama’a, dole ne kowace iri da za ta shigo kasar ta bi matakan doka da ka’idoji da ke tabbatar da cewa tana da aminci. Ya ce, dokokin da ake amfani da su wajen kula da GMOs ma sun fi tsauri fiye da na amfanin gona na gargajiya saboda an kara musu sinadaran halittu (genetic materials).
“Kafin a saki kowane irin amfanin gona domin a fara amfani da shi a kasuwanci, dole ne ta bi diddigin binciken halittu da sinadaran gina jiki sosai. Bayanai da ake da su a halin yanzu sun nuna cewa amfanin gona na GMO suna da lafiya, bisa sama da bincike 200 da aka gudanar a Turai, Amurka, Latin Amurka da wasu kasashen Afirka.
Shi ya sa aka amince a ci su, domin sun cika sharudan tsaro. Babu wani rahoto daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ko kuma Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) da ya nuna cewa amfanin gona ko abincin da aka sarrafa ta hanyar ilmin kwayoyin halitta (GMO) na da illa ga mutane ko dabbobi.
A halin yanzu akwai amfanin gona irin su masara, tumatir, shinkafa, waken suya da gwanda da aka sarrafa ta hanyar GMO a kasuwa. Babu wani tabbacin matsalar tsaro game da hakan.”
Adamu ya ce Nijeriya ba ta samar da isasshen abinci na gargajiya (organic) ba, sai dai amfanin gona na yau da kullum kamar sauran kasashe masu tasowa, inda manoma ke amfani da takin zamani, magungunan kashe kwari da sauran sinadarai.
Ya bayyana cewa amfanin gona na kwayoyin halitta (GM crops), an noman wasu daga cikinsu ne domin su iya jure matsalolin da manoma ke fuskanta a lokacin noman su, kamar kwari masu lalata shuka, irin su stem borer da kuma kwaron fall armyworm.”













