• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Warware Kalubalen Da Kiwon Kifi Ke Fuskanta A Nijeriya

by Abubakar Abba
2 years ago
Kifi

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

Tarihin kiwon Kifi a Nijeriya, ya faro ne karkashin shirin kiwon Kifi na gwamnati a gonakin  Panyam da ke garin Jos  babban birnin Jihar Filato a shekarar 1951, inda a yanzu ake tafiyar da gonakin a matsayin masu zaman kansu.

Bincike ya nuna cewa, kiwon Kifi hanya ce guda daya tilo wadda za a iya cike gibin da ake da shi na karancinsa tare da kara yawan wanda ake kiwatawa a fadin wannan kasa.

  • An Gudanar Da Bikin Reel Africa A Birnin Shanghai
  • Gwamnatin Kano Ta Dawo Da Ma’aikatan Da Ta Dakatar Da Ganduje Ya Ɗauka Aiki

Sakamakon wannan bincike ne, ya sa Nijeriya ta shiga harkokin kiwon Kifi gadan-gadan, musamman saboda karancinsa da ake samu a manyan rafi; sakamakon yawan kamun sa da ake yi da kuma kara samun masu bukatarsa da suke karuwa a wannan kasa.

Bukatar da ake da ita ta Kifi a Nijeriya, an kiyasata ta kai ta tan miliyan 2.97 a duk shekara, sai dai ana iya samar da Kifin da ya kai kimanin tan miliyan 1.07 ne kawai a duk shekarar.

Wannan na nuna cewa, ana da gibin da ya kai na kimanin tan miliyan 1.9, wanda za a iya fitar da shi zuwa kasashen ketare, domin sama wa  Nijeriya kudin shiga; wanda akalla zai iya tasamma kimanin dala biliyan 1.2.

Hatta tan mliliyan 1.07 da ake samu a duk shekara, ana kuma samar da Kifi kimanin tan miliyan 313,231 ne kacal, inda kuma ake samar da sauran Kifin da ya kai kimanin tan miliyan 759,828 a duk shekara ta hanyar kiwata shi.

Har ila yau, wasu daga cikin hanyoyin da za a rage kalubale ko matsalolin kiwon kifin sun hada da samar Da Kudade, wanda ko shakka babu babban kalubale ne ga babban bankin Nijerya (CBN), ta hanyar shirin bayar da dauki daban-daban da yake bayarwa na kiwon Kifi, domin samun ribar da ta doshi naira biliyan 21.

Kazalika, ta hanyar shirin nan na bunkasa kaya na (CDI), babban bankin Nijeriya (CBN), ya rabar da kimanin naira miliyan 500 ga kamfanoni 40  da kuma wasu daga cikin masu kiwon Kifi sama da 3,000.

Babu shakka, wannan dauki ya taimaka wajen kara samar da kimanin tan 200 a duk shekara, inda kuma gwamnatin tarayya ta hanyar sauran shirye-shiyen ta tallafa wa masu kiwon Kifi wadanda ke a fadin wannan kasa.

Bugu da kari, ta hanyar bayar da rance ta bankunan ‘DMBs’, gwamnatin tarayya ta amince da bayar da bashi ga masu kiwon Kifin a Nijeriya, musamman domin su kara habaka sana’ar tasu.

Sai kuma batun samo ingantaccen Iri na Kifin da za a kiwata: Yana da matukar muhimmanci ga duk wanda zai fara kiwon Kifi, ya tabbatar ya samo ingantaccen Iri na Kifin da zai fara kiwatawa tare da samar da kyakkyawan yanayin da ya dace.

Don haka, ya kamata gwamnati ta samar da wuraren gudanar da yin bincike a fannin kiwon Kifi tare da samar da wadatattun kayan aiki, domin rika samar da ingantaccen Kifi a kasar nan.

Haka zalika, akwai batun samar da ingantaccen kwamin kiwon Kifin: Irin kwamin kiwon Kifin da ya fi dacewa masu kiwon su fi yin amfani da shi sun hada da; wanda aka gina, ma’ana wanda ake yi a cikin roba ko kuma wanda na tafi da gidanka da sauran makamantansu.

Sa’annan, batun kula da lafiyar Kifin da ake kiwatawa: Rashin kula da yadda ake kiwon Kifin da kuma rashin ciyar da su abinci, na haifar musu da barkewar annoba tare da mutuwa. Za a iya samun wannan nasara ta hanyar kafa gidan gonar kiwon Kifi a wuraren da ke da ruwa mai kyau da tsafta.

Sai kuma tabbatar da daidaitacciyar kasuwa: Gazawa wajen samar da tabbatacciyar kasuwa na daya daga cikin babban kalubalen da fannin kiwon Kifi ke fuskanta a wannan kasa.

Fannin kiwon Kifi kamar fannin sauran noma ne, wanda ba zai iya samun nasara ba, idan har ba a samar da ingattacciyar kasuwar da kamata ba, musamman domin kai wa ga abokan cinikayya.

Haka nan, batun samar da ingantattun hanyoyin safafar Kifin: Ana bukatar a samar da ingattattun hanyoyi, don yin jigilar Kifin daga gonakin da aka kiwata su zuwa guraren da za a sayar da su.

Saboda haka, ana bukatar gwamnati ta tabbatar da inganta hanyoyi, musamman domin a rage wa masu kiwon Kifin tsadar kashe kudaden yin jigilar da kuma rage musu asara, sakamakon rashin hanyoyi masu kyau.

Bugu da kari, batun samar da wajen adana Kifin, wato firji mai Inganci: Ana bukatar a samar da firjin da za a rika adana Kifin da za a yi jigilarsu, don gudun ka da su lalace.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
Noma Da Kiwo

Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci

November 2, 2025
Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya
Noma Da Kiwo

Sharhi Kan Noman Agwaluma A Nijeriya

October 18, 2025
‘Yansanda Sun Cafke Ɓarayi 13 Tare Da Ƙwato Shanu 27 A Kaduna
Noma Da Kiwo

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Ayyana Yi Wa Kasuwannin Sayar Da Dabbobi 9 Garanbawul

October 18, 2025
Next Post
Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa

Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

“Ƴan Adawa Sun Wuce Gona da Iri — Wike Ya Soki Masu Goyon Bayan  Trump

November 3, 2025
Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

Shugabannin Wasu Kasashe Za Su Halarci Baje Kolin CIIE Karo Na Takwas A Birnin Shanghai

November 3, 2025
Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

Li Qiang Zai Halarci Bikin Bude Taron CIIE Na 8 Da Sauran Ayyuka

November 3, 2025
Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya

November 3, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

Bikin Baje Kolin CIIE Zai Samarwa Najeriya Karin Damammaki

November 3, 2025
Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro

November 3, 2025
Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

Sin Ta Yi Allah Wadai Da Illata Fararen Hula Tare Da Fatan Gaggauta Kawo Karshen Yaki A Sudan

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.