Daya daga cikin ma shirya zanga-zangar da ake yi saboda matsin tattalin arziki, Damilola Adenola, ya bayyana cewa masu zanga-zangar ba su cimma burinsu ba tukuna.
A wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan Talabijin ɗin Channels TV a jiya Juma’a, Adenola ya jaddada cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kamata ya yi wa ƴan Nijeriya jawabi kai tsaye idan ya damu da walwalarsu.
- Ƴansanda Sun Kama Mutane 64, Sun Ƙwato Buhun Taki 693 Daga Masu Zanga-zanga
- Ku Ci Moriyar Damarmakin Da Gwamnatin Tinubu Ta Samar Maimakon Zanga-zanga – Minista
Adenola ya ƙaryata zargin cewa an ƴan siyasa sun ɗauki nauyin zanga-zangar, yana cewa, “Zanga-zangar ra’ayin ‘yan Nijeriya ne da ke cikin matsin ƙuncin tattalin arziki. Masu zanga-zangar ba su cimma burinsu ba tukuna, waɗanda aka bayyana a cikin ƙudirinsu. Amma abin da muka yi shi ne aika sako mai ƙarfi ga waɗanda ke riƙe da madafun iko.
Sun ga abin da mutane za su iya yi don bayyana rashin jin daɗinsu. Wannan ya samun taɓi ne kuma za a ci gaba. Muna jiran gwamnati ta amsa buƙatunmu. Kafin wannan, zanga-zangar za ta ci gaba.”
Ya kara da cewa, wannan zanga-zangar zai sanya gwamnati ta fahimci cewa mulki na mutane ne. Masu ɗaukar nauyin wannan zanga-zanga su ne yunwa da rashin tsaro. Shi ne rashin daidaito na tattalin arziki da haihuwar farashin kaya.