Hukumar Gudanarwar Kamfanonin Ɗangote, ta yaba wa Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC), bisa yadda take gudanar da ayyuka daban-daban; a kan buƙatun da kamfanin mai yake da shi na samar da ɗanyen mai daga Kamfanonin Mai na Duniya (IOCs), tare kuma da samar da dokoki da tsare-tsaren hada-hadar ɗanyen mai na cikin gida, wanda zai bad a damar aiwatar da gaskiya a kamfanonin mai.
Mataimakin Shugaban Kamfanin Man Fetur da Gas na Kamfanin Ɗangote, Mista Edwin ya bayyana cewa; “Idan aka gabatar da sharuɗɗa tare da ƙa’idojin sayar da ɗanyan man fetir a cikin gida yadda ya kamata, hakan na tabbatar da cewa; za mu yi hulɗa kai tsaye tare da kamfanonin da ke haƙo ɗanyen mai a Nijeriya kamar yadda dokar kamfanoni man fetur (PIA) ta gindaya.”
Edwin ya ƙara da cewa, Kamfanonin Mai na Duniya (IOCs), da ke aiki a Nijeriya; sun ta faman yi wa buƙatun wannan kamfani zagon ƙasa, kan buƙatar samar da ɗanyen mai tare da tace shi a cikin gida.
Ya ci gaba da bayyana cewa, idan aka bai wa kamfanin man dakon kaya ta hannun ‘yan kasuwa, wani lokacin farashin ya kan kai dala biyu zuwa dala huɗu (kowace ganga), sama da farashin da Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ta ƙayyade.
“Misali, mun biya dala 96.23 kan kowace ganga ta kayan ɗanyen man Bonga a watan Afrilu (ban da kuɗin sufuri). Farashin ya haɗa da dala 90.15 da kuma dala 5.08 na Kamfanin Albartun Mai na Nijeriya NNPC da kuma dala ɗaya na ‘yankasuwa. Saboda haka, a cikin wannan watan; mun samu damar sayen WTI a kan farashin dala 90.15 da kuma dala 0.93 ciki har da kuɗin sufuri. A lokacin da Kamfanin NNPC ya rage farashinsa, sakamakon yadda kasuwa ta tabbatar da cewa farashin ya yi yawa, sai wasu daga cikin ‘yan kasuwa suka fara neman kimanin dala miliyan huɗu a hannunmu, sama da na kamfanin ɗaukar kaya na ‘Bonny Light’.”
Har ila yau, bayanan kafafen sadarwa sun nuna cewa; farashin da ake ba mu, ya fi farashin kasuwa kamar yadda muke ji ko bibiyar waɗannan kafafen sadarwa ko dandamali. Kwanan, dole ta sa muka sanar da Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC)”,
Edwin ya ce, ya kuma buƙaci hukumar da ta sake duba batun farashin.
Martanin na Edwin, ya zo ne daidai lokacin da wata sanarwa; wadda Babban Jami’in Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriyan (NUPRC), Injiniya Gbenga Komolafe; a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin ARISE, inda yake cewa; “kuskure ne mutum kamfanonin mai na ƙasashen waje sun ƙi samar da ɗanyen mai ga masu tacewa na cikin gida, kamar yadda dokar masana’antar mai ta tanadar, akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin mai saya da mai sayarwa.”
Edwin ya bayyana cewa, “Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriyan (NUPRC), ta taimaka wa matatar mai ta Ɗangote ƙwarai da gaske, domin kuwa sun taka muhimiyar rawa don taimaka man wajen samun ɗanyan mai. Duk da haka, akwai yiwuwar wasu ne suka yi wa Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriyan (NUPRC) kuskure, shi ya say a yi wannan furuci na cewa, an ƙi sayar mana. Don saita bayanan daidai, muna so mu sake fito da bayanan dalla-dalla a ƙasa.
“Baya ga Kamfanin Kula da Albakatun Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), har zuwa yau ɗin nan; daga hannun wani mai samar da mai a ƙasar nan shi kaɗai muka sayi ɗanyan man fetur (Sapetro). Duk sauran masu hada-hadar man, na tura mu ne ga abokanan kasuwancinsu na waje.
“Waɗannan masu gudanar da kasuwanci a waje, babu wani abin da suke tsinanawa a matsayinsu na waɗanda ke zaune a ƙasashen waje, illa samun rarar man fetur ɗin da ake samarwa da kuma wanda ake amfani das hi a Nijeriya. Ba a yi musu hukunci da dokokin Nijeriya, sannan ba sa biyan haraji a Nijeriyan a kan wannan rara da ba ta dace ba; suke kuma samu.
“Sashen ciniki na ɗaya daga cikin abubuwan da Kamfanonin Mai na Duniyar (IOCs), suka ƙi yarda a sayar mana kai tsaye, inda aka nemi mu nemo waɗanda za su a tsakiya, a sayar musu sai su kuma su sayar mana. Don haka, mun yi tattaunawa da su ta kusan wata tara, amma a ƙarshe said a muka dangana zuwa Kamfanin Kula da Albakatun Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), wanda ya taimaka wajen warware matsalar,” in ji Edwin.
A cewarsa, “Lokacin da muka dangana zuwa kasuwa don sayen ɗanyen man da muke buƙata a watan Agusta, waɗannan masu harkokin kasuwanci a waje cewa suka yi da mu, sun shigo da kayansu Nijeriya a jirgin ɗaukar kaya na Pertamina (mallakin kamfani mai na ƙasar Indunisiya), amma mu ɗan jira mu ga abin da zai faru.
“Wannan ba shi ne karo na farko ba, ya sha faruwa musamman a kan ɗanyen man da muke so saya, amma sai a sayar wa da matatar mai ta Indiya ko wasu daga cikin ƙasashen Asiya tun kafin ma a raba kayan a hukumance a taron rage farashin da Kamfanin Kula da Albakatun Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ke jagoranta.
“Duk da haka, muna buƙatar Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriyan (NUPRC), ta sake duba batun farashin. Domin kuwa, hukumar ta yi iƙrari da dama na cewa; ya kamata ciniki ya kasance a kan tsarin mai saye da mai sayarwa. Duk da haka, ƙalubalen shi ne; taɓarɓarewar kasuwanci, ta hanyar samun masu saye da dama da kuma masu sayarwa su ma da yawa duk a lokaci guda. Inda kuma a gefe guda matatar man fetur ke buƙatar yin lodi na ɗanyan man fetir a daidai wannan lokaci, sai ga shi kuma an bai wa mutum shi kaɗai a gefe.
“Don kaucewa hauhawar farashin kayayyaki a kasuwa, wajibi ne a samar da iskar gas a cikin gida tare da ƙayyade adadin yadda masu samar da shi za su samar, wanda hakan zai taimaka wajen ƙayyade farashinsa”, in ji Edwin.