Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Ruben Amorim ya ce kungiyar tasa na nan da farin jininta ga ‘yan wasa duk da matsayi na 14 da take yanzu a teburin Premier League kuma har yanzu manyan ‘yan wasan duniya suna son buga wa kungiyar wasa duk da halin rashin kokarin da kungiyar take a wannan lokacin.
Amorim, dan kasar Portugal da ya fara horar da Man United a watan Nuwamba ya ce “ya san” abin da yake game da tawagar tasa a kakar wasa mai zuwa. Manchester United na neman dan wasan Brazil mai taka wasa a Wolbes, Matheus Cunha, da kuma alakanta ta da ake yi da danwasnan kungiyar Ipswich Town Liam Delap, wanda yake da farashin fan miliyan 30 a kwantaraginsa.
- Mataimakin Shugaban Ƙasa Zai Wakilci Nijeriya A Rantsar Da Shugaban Gabon
- Shugaban INEC Ya Yi Kira Da A Sake Fasalin Tsarin Zabe Gabanin 2027
Manchester United na bukatar ta lashe kofin zakarun Turai na Europa League kafin ta samu gurbi Kofin Zakarun Turai a kaka mai zuwa sai dai Amorim ba shi da wata tantama cewa farin jinin kungiyar na nan duk da hakan.
“Manchester United ce fa kowane dan wasa na hankoron taka wasa a cikinta kuma idan kuka duba kungiyar a yanzu, kamar akwai matsaloli, ciki har da sauya koci da aka yi amma duk da haka muna da masaniyar abin da ya kamata, kuma abu ne mai sauki a ganar da dan wasa” in ji Amorim, wanda ya koma United daga Sporting Lisbon.
Ya kara da cewa magana ce ta karshen kaka kuma komai zai iya sauyawa. Amma dai suna so su fara komai da wuri kuma sun san yadda za su yi hakan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp