Yau dai sama da shekaru 70 da suka wuce ke nan da wasu kasashen Asiya da Afirka suka bude babin yakar mulkin mallaka da ra’ayin nuna fin karfi bisa ruhin taron Bandung da ya yi kiran “hadin kai da sada zumunta da hadin gwiwa”, taron da ya samu halartar kasashe 29 na Asiya da Afirka, wanda ya gudana a birnin Bandung na kasar Indonesia. A zamanin da muke ciki kuma, kasashe masu tasowa na ci gaba da rungumar ruhin taron, a kokarinsu na gyara tsarin duniya, wato a kafa tsarin da ke tabbatar da bunkasar kasa da kasa ta bai daya, tare da yin watsi da tsohon tsarin da kasashe masu karfi ke cin zalin kasashe masu karamin karfi.
A gun taron Bandung, wakilin kasar Sin ya jaddada cewa, “kamata ya yi kasa da kasa komai karfinsu su yi zaman daidaito da juna”, furucin da ba kawai ya yi watsi da mulkin mallaka ba ne, hatta ma da irin yadda kasashe masu ci gaba ke nuna fin karfi a harkokin duniya. A gwagwarmayar da kasashe masu tasowa suka yi cikin shekaru 70 da suka wuce, sun karya lagon babakeren da aka kafa ta dalar Amurka, inda kasashen Brazil da Sin suka yi cinikin waken soya da kudadensu, kuma India ta sayi man Iran da kudinta na Rupee, kasashen Afirka ma na kokarin sa kaimin kafa tsarin ciniki na kudadensu a yankin ciniki marar shinge na nahiyar, matakan da suka sa kason cinikin da aka yi da dala ya ragu daga kashi 73% a shekarar 2001 zuwa kashi 49% a yanzu. Baya ga haka, kasashen sun kuma karya babakeren da aka yi ta fannin kimiyya da fasaha, inda kasar Sin ta fitar da samfurin kirkirarriyar basira ta Deepseek, kuma Masar ta kafa masana’antar samar da motocin lantarki ta farko a Afirka…… A sa’i daya kuma, kasashen sun kara fitowa da muryoyinsu a duniya, duba da cewa, tarayyar Afirka ta sa kaimin ganin gyare-gyaren hukumomin hada-hadar kudi na duniya bayan da aka shigar da ita kungiyar G20, kuma a gun shawarwari kan sauyin yanayin duniya kungiyar G77 ta bukaci kasashen yamma su biya diyyar hasarorin da suka sha……
Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai wasu kasashe uku na kudu maso gabashin Asiya a wannan mako, ta kuma kara shaida yadda ake ci gaba da rungumar ruhin taron Bandung. A ziyararsa a Vietnam, kasashen biyu sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa har 45, tare da fitar da hadaddiyar sanarwar cewa, za a yayata akidun zaman lafiya da ci gaba da adalci da dimokuradiyya da ‘yanci da baki dayan dan Adam ke rungumarsu, tare da nuna goyon baya ga bunkasar kasashe daban daban da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya. A Malaysia kuma, kasashen biyu sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ke cewa, za su karfafa hadin gwiwarsu ta fannin more damammaki da tabbatar da ci gaba da tinkarar kalubale da kiyaye tsaro, tare da bayar da karin gudummawarsu wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da inganta tsarin hadin gwiwa a shiyyar. Har ila yau, a kasar Cambodia kuma, kasashen biyu sun daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa ta fannin aiwatar da ayyuka masu alaka da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, baya ga hadaddiyar sanarwar da suka fitar ta jaddada muhimmancin “ka’idoji biyar na zaman tare cikin lumana” da kuma ruhin taron Bandung. Wadannan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da suka cimma da sanarwoyin da suka fitar duk sun shaida ainihin sakon da taron Bandung ke fatan isarwa, wato hakkin ci gaba shi ne hakkin dan Adam mafi muhimmanci, kuma ‘yancin gudanar da harkoki na kashin kanta shi ne tushen ikon mulkin kai na duk wata kasa, kuma matukar kasa da kasa suka zama tsintsiya madaurinki guda za su iya tinkarar kalubalen da ke gabansu.
A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna fin karfi a tarihin wayewar kan dan Adam. (Lubabatu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp