Fitaccen Jarumin nan da ya shafe tsahon shekara ashirin da bakwai cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Jarumin da ke ci gaba da haskawa a cikin sabbin fina-finai masu dogon zangon da ke fita a yanzu AUWAL ISAH WEST, ya yi bayani dangane da abin da ya shafi rayuwarsa da kuma harkarsa ta fim. Ga dai tattaunawar tare da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:
Ya sunan Jarumin?
Sunana Auwa Isah West.
Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka?
Ni dan asalin Jihar Kano ne, Mamata ‘yar Kura ce, Babana dan Garko Jihar Kano ne, daga bisani aiki ya kai Babana Jihar Filato. Na yi karatuna a garin Jos, bayan babana ya rasu na dawo garin Kano wajen ‘Yan’uwana. Bayan nan sai na shiga harkar fim dalilin Ali Nuhu shi ne maigida na.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar fim?
Eh! Toh, ina sha’awar abun ne kawai.
Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance?
Ban sha wata wahala ba, saboda ina da maigidana Ali Nuhu kuma ta dalilinsa na shiga.
Za ka yi kamar shekara nawa da fara fim?
Zan kai kamar shekara Ashirin da bakwai (27) da farawa.
Ko akwai wani kalubale daka fuskanta wajen iyaye, musamman lokacin daka fara sanar musu kana son shiga masana’antar?
Allahamdulillah ban taba samun wani kalubale ba ‘because I’m the best’.
A wanne fim ka fara fitowa?
Na fara da fim din Zubaida.
Da wanne Jarumi da Jaruma kuka fito cikin fim din, kuma wanne rawa ka taka cikin fim din, kuma ya karbuwar fim din ta kasance?
Na fito tare da Ahmad S.Nuhu da sarki Ali Nuhu da Abida Muhammad. Gaskiya fim din ya samu karbuwa sosai a kasuwa.
Bayan da ka samu nasarar shiga cikin masana’antar, wanne irin kalubale ka fara cin karo da shi?
Toh! gaskiya ban samu wani kalubale ba, because ni na zo da zuciya daya, kuma Allah ya bani sa’a saboda na dauke ta sana’a, sabanin wasu ba haka suka dauka ba.
Bayan da ka shafe tsawon shekaru fa, ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta?
Akwai gaskiya, wasu ba su dauke mu a matsayin wasu mutane kamar kowa ba, ‘Sometimes’ ma in mun je neman aure iyayen yaran suna mana ganin mutanen banza, shi ne kawai.
Wadanne irin nasarori ka samu game da fim?
Na samu nasarori sosai ina gode wa Allah, kuma ina gode wa maigidana Ali Nuhu.
Ya ka dauki fim a wajenka?
Na dauki fim babbar sana’a, duk abin da na samu a rayuwata daliln fim ne, so ina mai gode wa Allah sosai.
Me kake son cimmawa game da fim?
Ina fatan nima in samu wani dama da zan taimaki wasu kamar yadda aka yi min.
Bayan fim kana wata sana’ar ne?
Ina harkar mota, kuma ina da shagon kaya.
Kwanakin baya can masu kallo sun daina jin duriyarka, daga bisani kuma kwatsam sai ga shi ka dawo a wannan lokacin, me ya faru?
Toh! Dalilin hakan na je karo ilmi a ‘South Africa’ ne shiyasa.
Da yawan fina-finan da kake fitowa, ka fi fitowa a dan daba, wanda hakan ke sa wasu mutanen ke yi maka mummunan kallo, shin kai kake zabar hakan, ko kuwa labari ne ya ke zabarka?
Gaskiya ba haka bane, ba ni nake zabar hakan ba, labari ne yake zuwa da haka amma ina jin dadin hakan.
Ko za ka iya tuna adadin fina-finan da ka yi?
Gsky suna da yawa ba zan iya tunawa ba.
A gaba daya fina-finan da kayi wanne fim ka fi so, wanda ya zamo bakandamiyarka?
Kowanne fim ina so, amma na fi san ALAKA fim din Maigidana Ali Nuhu.
Bayan fitowa da kake matsayin Jarumi, shin kana rubuta labari, ko Bada umarni, ko shiryawa da sauransu, ko iya aktin kawai kake yi?
Eh! toh ina acting da kuma products.
Da wanne Jarumi ko Jaruma ka fi so a hada ka a fim kuma me ya sa?
Gaskiya ina jin dadin aiki da kowa, amma na fi jin dadin aiki da maigidana Ali Nuhu ‘because he’s so nice’.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin hakan, wanda ba za ka taba iya mantawa da shi a rayuwa ba?
Gaskiya akwai, mun taba zuwa Katsina ni da maigidana Ali Nuhu gidan wata mata take cewa “Ali mai ya hada ka da wannan mugun, ya bata ma shiri…”, sai oga na ya ce “ai fim ne Hajiya shi din na hannun damana ne” kuma ya kara da cewa ya fi sona a duk yaransa.
Ya batun aure, shin akwai ko kuma tukunna dai?
Eh! ina da aure yarana biyu Mace da Mamiji na yi wa ogana Ali Nuhu takwara.
Idan na fahimce ka a cikin masana’antar Kannywood Ali Nuhu shi ne ubangidanka, kamar yadda kowa ya ke da ubangida?
Eh! Sosai ma har ya wuce matsayin Ubangida masayin uba yake a guna shi ne Sarki Ali Nuhu.
Wanne irin matsaloli kuka fi fuskanta a cikin masana’antar, kuma ta wacce hanya kake ganin za a bi a gyara?
Rashin hadin kai da raina na gaba da kai. Eh! toh, kira na anan shi ne, mu ruke juna kuma mu ji tsoran Allah a duk inda muke, mu sani mu wakilan al’umma ne.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Burina game da fim bai wuce na Allah ya bani sa’a ni ma in rinka fim na kaina ba.
Wanne kira za ka yi ga masu kokarin shiga cikin masana’antar har ma da wadanda suke ciki?
Toh su yi hakuri saboda akwai wahala, so dole sai sun yi hakuri.
Me za ka ce ga makaranta wannan shafi na RUMBUN NISHAdI?
Ina yi wa kowa fatan alkhairi da wannan gidan Jarida Allah ya sa ku fi haka.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Toh ina mai godiya da wannan dama da kuka bani ina muku fatan alkhairi Allah ya sa kufi haka.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaida kowa da kowa masoyana na duniya gabaki daya.
Muna godiya ayi sallah lafiya
Ni ma na gode.