Wani rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, ya fitar ya nuna cewa hare-haren ‘yan bindiga a Nijeriya sun ragu da kashi 1.6 cikin 100 a watan Disamban 2024.
A rahoton, an bayyana cewa aƙalla mutum 708 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka yi garkuwa da mutane 674.
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
- Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Makaranta Kyauta Ga Dalibai 789,000
Haka kuma, wasu 671 sun mutu sakamakon rikice-rikicen tsaro a sassan Nijeriya.
Rahoton ya jaddada cewa duk da raguwar yawan hare-haren, yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na ci gaba da zama wuraren da aka fi samun tashin hankali.
Hakan ya biyo bayan yaÆ™in da ake yi da ‘yan bindiga, wanda ke nuna tasiri wajen rage hare-hare, amma har yanzu akwai buÆ™atar duba tushen matsalar tsaro.
Sai dai har yanzu akwai taɓarɓarewar tattalin arziƙi, ƙalubalen muhalli, da rashin shugabanci mai kyau.
Rahoton ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen samar da ayyukan yi ga matasa, magance matsalolin talauci da rashin ilimi, tare da ƙarfafa sojoji da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da kwanciyar hankali a dukkanin sassan ƙasar.
Ya zuwa yanzu, rahoton ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara zuba jari a fannoni kamar ilimi, lafiya, da kuma gyaran tattalin arziƙi domin rage dalilan da ke haifar da rikici a ƙasar.