ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hare-haren ‘Yan Bindiga Sun Ragu A Watan Disamban 2024, Amma Har Yanzu Ana Fuskantar Barazana – Rahoto

by Sadiq
2 years ago
Bindiga

Wani rahoto da kamfanin Beacon Security and Intelligence Limited, ya fitar ya nuna cewa hare-haren ‘yan bindiga a Nijeriya sun ragu da kashi 1.6 cikin 100 a watan Disamban 2024.

A rahoton, an bayyana cewa aƙalla mutum 708 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka yi garkuwa da mutane 674.

  • Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
  • Gwamnatin Kano Ta Raba Kayan Makaranta Kyauta Ga Dalibai 789,000

Haka kuma, wasu 671 sun mutu sakamakon rikice-rikicen tsaro a sassan Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya jaddada cewa duk da raguwar yawan hare-haren, yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas na ci gaba da zama wuraren da aka fi samun tashin hankali.

Hakan ya biyo bayan yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga, wanda ke nuna tasiri wajen rage hare-hare, amma har yanzu akwai buƙatar duba tushen matsalar tsaro.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Sai dai har yanzu akwai taɓarɓarewar tattalin arziƙi, ƙalubalen muhalli, da rashin shugabanci mai kyau.

Rahoton ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen samar da ayyukan yi ga matasa, magance matsalolin talauci da rashin ilimi, tare da ƙarfafa sojoji da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da kwanciyar hankali a dukkanin sassan ƙasar.

Ya zuwa yanzu, rahoton ya bayyana cewa akwai buƙatar ƙara zuba jari a fannoni kamar ilimi, lafiya, da kuma gyaran tattalin arziƙi domin rage dalilan da ke haifar da rikici a ƙasar.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sojoji Sun Fara Binciken Kuskuren Kashe Fararen Hula Da ‘Yan Sa-kai A Zamfara

Sojoji Sun Fara Binciken Kuskuren Kashe Fararen Hula Da 'Yan Sa-kai A Zamfara

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.