Akalla yara 3,000 ne hare-haren ‘yan bindiga ya yi sanadin daina zuwansu makaranta a wasu kauyukan Karamar Hukumar Jibia a Jihar Katsina.
Sa’ad Salihu, shugaban sansanin ‘yan gudun hijira ne, ya bayyana hakan yayin wata ziyara da manema labarai suka kai yankin a ranar Litinin.
- Dole Burtaniya Ta Shirya Yaki Da Rasha – Sojin Burtaniya
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban NULGE Reshen Zamfara Mai Dauke Da Juna Biyu
Salihu, wanda kuma shi ne shugaban Kungiyar Ci gaban Matasa ta Shimfida, ya ce wasu daga cikin yaransu na zuwa makaranta kafin al’ummar yankin su tsere sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan gudun hijirar, wadanda a halin yanzu suke makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke Jibia, sun fito ne daga al’ummomin Kwari, Zango, Shimfida, Tsauni, Far Faru, Tsambe da Gurbin Magariya.
A cewarsa, babban koma baya ne a fannin ilimi, sakamakon yawan yaran da ‘yan bindiga suka kore su daga makaranta, inda ya ce sama da ‘yan gudun hijira 15,000 ne a sansanin.
“Akalla mata da kananan yara 23 ne suka mutu a sansanin a cikin watanni hudu, ko dai sakamakon hauhawar jini ko kuma damuwa, yayin da mata 35 su ka haihu.
“Sama da yara 3,000 da ke sansanin a halin yanzu ba sa iya samun ilimi a halin yanzu.”
“Daga al’ummar Shimfida kadai, muna da mutane 8,000 da ke wannan sansanin; al’ummar FarFaru, sama da 7,000 da kusan 200 sun fito ne daga al’ummar Zango.