Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin.
Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu.
- NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas
- Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu
Ta bayyana cewa haɗin gwuiwar Ƴansanda, da Sojoji, da Jami’an sa-kai da mafarauta ya fatattaki maharan tare da dawo da zaman lafiya, inda yanzu aka fara sumame don kamo su. A ranar Lahadi, kwamishinan Ƴansanda Adekimi Ojo da Daraktan DSS na jihar sun ziyarci Babanla don tantance halin tsaro, tare da ganawa da Sarkin garin, Oba Yusuf Aliyu Alabi Arojojoye II.
Kwamishinan ya bayar da umarnin ci gaba da sintiri da tattara bayanan sirri tare da tura ƙwararrun jami’an bin sawu, yayin da DSS ta yi alƙawarin bayar da goyon baya da bayanan sirri domin kama duk masu hannu a harin. An kuma roƙi jama’a su kwantar da hankula, su kasance masu lura, tare da bayar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp