Maren Aradong, Hakimin Kauyen Hurti da ke karamar hukumar Bokkos a Jihar Filato, ya yi zargin cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane 40, sun kona gidaje 383 tare da raba fiye da mazauna 1,000 da muhallansu yayin wani hari da suka kai.
Mista Aradong ya bayyana haka ne a lokacin da sakataren gwamnatin jihar, Samuel Jatau, ya jagoranci wasu jami’an gwamnati a ziyarar tantance irin barnar da ‘yan bindigar suka yi wa al’ummar yankin a ranar Lahadi a Jos.
- Kicibus: An Gabza Yaki Tsakanin Yan Bijilanti Da ‘Yan Fashi, Sun Kashe Barayi 30 A Zamfara
- Sin Ta Gabatar Da Dabarunta Na Raya Sana’o’i Da Fasahohi Masu Kiyaye Muhalli Ga Taron WTO
A ranar 2 ga Afrilu, ‘yan bindiga sun kai hari a Hurti, Josho, Daffo, da sauran al’ummomin yankin.
Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana hare-haren baya-bayan nan da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jihar a matsayin shirin masu nufin tada zaune tsaye da kawo cikas ga zaman lafiyar jihar ne a maimakon a alakanta harin da rikicin manoma da makiyaya.
Da yake karin haske kan lamarin, Mista Aradong ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da kayan abinci da sauran kayayyaki.
Mista Aradong, wanda ya yabawa gwamnatin jihar da jami’an tsaro bisa fara gudanar da binciken gaggawa da suka yi, ya kuma bukaci a kara tura jami’an tsaro a yankunan da lamarin ya shafa.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Mista Jatau, wanda ya jajanta wa iyalan da suka rasa ‘yan uwansu yayin harin, ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kuma bayar da tallafi ga wadanda lamarin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp