Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta hanyar sashin haɗin gwuiwa na Operation Haɗin Kai (OPHK), ta kai hare-haren sama da suka hallaka a ƙalla ƴan ta’adda 15 a jihar Borno.
Kakakin rundunar, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa hare-haren sun gudana ne a ranar Laraba, 3 ga Satumba 2025. Ya ce an kai harin ne kan sabuwar mafakar ƴan ta’adda da aka gano a yammacin garin Zuwa da ke cikin dajin Sambisa.
- Mutum 2 Sun Shiga Hannu Kan Sace Adaidaita Sahu A Borno
- ‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno
A cewar shi, an samu sahihin bayanan sirri da kuma binciken jiragen leƙen asiri kafin a kaddamar da harin, wanda ya yi sanadiyar hallaka ƴan ta’adda da dama ciki har da wasu shugabanninsu tare da rusa gine-ginen da suke amfani da su.
Sanarwar ta ƙara da cewa nasarar wannan hari ta sake tabbatar da ƙudirin NAF na kare rayuka da dukiyoyin ƴan Nijeriya, tare da tallafawa dakarun ƙasa wajen murƙushe cibiyoyin ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp