Al’ummar kauyen Tunburku da ke unguwar Kidandan a Karamar Hukumar Giwa a Jihar Kaduna, sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin dadinsu kan yadda ‘yan bindiga da suka addabi yankin.
Masu zanga-zangar da suka hada da matasa da tsofaffi, sun yi tattaki zuwa fadar masarautar Zazzau da ke Zariya.
- Ba Wa Matasa Ilimi Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro – Tinubu
- Za A Rataye Mutane 2 Sakamakon Kashe Dan Acaba A Adamawa
Malam Yusuf Jibrin, wanda ya yi magana a madadin al’ummar yankin, ya bayyana irin abubuwan da al’ummar ke fuskanta a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga.
Ya bayyana yadda hare-haren ‘yan bindiga ke gurgunta ayyukan noma da tattalin arziki, sannan yake haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron daukacin al’ummar yankin.
Malam Amiru Abubakar, wani mazaunin garin, ya bayyana irin ta’asar da ‘yan bindiga ke yi ta hanyar kashe-kashe da sace-sace da kuma karbar haraji ga manoma don neman izinin yin noma.
Ya kara bayyana irin yadda mata ke fuskantar cin zarafi fyade da kuma sace-sacen dabbobi, wanda hakan ya sa gidaje da dama ba su da isasshen abinci.
“Suna sace mana dabbobi kuma sun dauke mu kamar bayi,” Abubakar ya koka.
A martaninsa, Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, yayin da yake jajanta wa al’ummar, ya bayyana cewa ya sha samun irin wadannan rahotanni daga yankin.
“A gaskiya lamarin tsaro a Karamar Hukumar Giwa yana hana mu barci,” in ji Bamalli.
Sarkin ya tabbatar wa al’ummar jihar zai jajirce don ganin an magance matsalolinsu.
Ya yi alkawarin mika lamarin ga hukumomin da abin ya shafa domin daukar matakin da ya dace da gaggawa.