A wani lamari mai kayatarwa da jarumtaka, rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta yi nasarar dakile hare-haren ‘yan bindiga guda biyu, tare da ceto matafiya mutane 18 da aka sace tare da kwato wasu dabbobi a wani hari kuma na daban.
Hare-haren da suka faru a ranar 3 ga Janairu, 2025, sun nuna irin kokarin da rundunar ‘yansandan Katsina ke yi na tabbatar da tsaro a fadin jihar.
- NPA Ta Buƙaci A Yi Nazari Kan Tsarin Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa Na Ƙasa Da Ƙasa
- Sakataren Gwamnatin Ondo Ya Rasu Bayan Hatsarin Mota
A cewar kakakin rundunar ‘yansandan, Sadiq Abubakar, ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK-47 sun yi wa wasu motoci hudu kwanton bauna kan hanyar Funtua zuwa Gusau, kan hanyar zuwa kauyen Yankara da wasu kuma Uku kuma sun fito daga Gusau.
Da yake amsa kiran gaggawa, shugaban rundunar ‘yansanda na Faskari (DPO) cikin gaggawa ya taso tawagarsa zuwa wurin.
Bayan artabu da ‘yan bindigar, jami’an sun tarwatsa ‘yan bindigar tare da ceto dukkan fasinjoji 18 ba tare da wani ya samu wani rauni ba.
Bugu da kari, Abubakar ya kara da cewa, a yammacin ranar da misalin karfe 11 na dare wasu ‘yan bindiga sun kuma sake kai wani hari kauyen Gidan Gada da ke karamar hukumar Kafur a jihar.
‘Yan Ta’addan sun tattaro shanu da dama tare da yin yunkurin tserewa da su.
A bisa bayanan sirri, tawagar jami’an hadin gwiwa daga Kafur da hedikwatar ‘yansanda ta Malumfashi sun bi sahun ‘yan ta’addan zuwa kauyen Fanisau.
Jami’an sun sake fafatawa da ‘yan bindigar, inda suka yi nasarar kwato dukkan dabbobin da suka sace.
Sai dai a yayin artabun, DPO na Kafur ya samu raunin harbin bindiga.
Nan take aka garzaya da shi asibiti, inda aka ce yana cikin koshin lafiya kuma yana karbar magani.
Kwamishinan ‘yansandan jihar Katsina, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yabawa jami’an bisa jajircewarsu da kishinsu na ganin bayan ‘yan ta’adda a jihar.